Wani Uba da Ke Renon Jaririyarsa Ya Nannade Ta Cikin jaka Bayan da Ta Totsa Toroso, Bidiyon Ya Jawo Cece-Kuce

Wani Uba da Ke Renon Jaririyarsa Ya Nannade Ta Cikin jaka Bayan da Ta Totsa Toroso, Bidiyon Ya Jawo Cece-Kuce

  • Wani uba da ke renon wata jaririyarsa ya gamu da jarrabawarsa ta farko yayin da diyar tasa ta totsa toroso
  • A wani bidiyon da Michelle Andrus yada a TikTok, an ga lokacin da uban ke kokarin nade yarinyar a cikin jakar leda
  • Alamu na nuna kamar mutumin bai san yadda ake kula da yara ba, mutane da dama sun yi martani a kafar TikTok

Wani bidiyon da aka yada na mahaifin da ke renon diyarsa ya yadu a intanet, akalla mutane miliyan 3.3 ne suka kalla, mutum 92k ne suka yi dagwale.

A bidiyon da Michelle Andrus ya yada, an ga lokacin da mahaifin ke kokarin jigilar kula da jaririyar cikin halin rashin kwarewa.

A bidiyon da aka yada a ranar Juma'a 25 ga watan Nuwamba, mahaifin ya dauki mataki yayin da yarinyar ta totsa toroso a kunzugun da ke jikinta, har yana fitowa ta baya.

Kara karanta wannan

Mahaifiyata Nake Taimakawa, Mahaifinmu Yayi Watsi Damu, Bidiyon Yarinya Mai Shekaru 15 da Talla

Yadda uba ke kula da diyarsa a cikin gida ya ba da mamaki
Wani Uba da Ke Renon Jaririyarsa Ya Nannade Ta Cikin jaka Bayan da Ta Totsa Toroso, Bidiyon Ya Jawo Cece-Kuce | Hoto: TikTok/@mandrus0920.
Asali: UGC

Yadda uban ya nade diyarsa a jaka

Mutumin ya natsu wajen tabbatar da ya nade yarinyar a jaka, amma ya kula sosai ta yadda bai bari ya jefa ta gaba daya a jakar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon mai dakiku 16, alamu sun nuna yarinyar ta fahimci akwai matsala, duba da yadda fuskarta ya nuna.

An ga yarinyar na tsilli-tsilli da idanu kamar dai tana neman bahasin abin da ke faruwa.

Mutane sama da 3k ne suka yi martani kan bidiyon, inda suka bayyana abin da ya taba faruwa dasu a matsayin iyaye.

Martanin jama'a

Jama'a da dama sun yi martani, amma ga kadan daga abin da muka tattaro muku:

@user1315621561974 yace:

"Ta rude gaba daya, kamar mai tambayar meye na yi ne?"

@Becki_Boof tace :

"Ta yi irin...na matsa lamba sosai."

@Toya yace:

Kara karanta wannan

Kanwar Maza: Bidiyon Tarairayar da ‘Yan Uwan Amarya Maza 7 Suka yi Mata Wurin Aurenta ya Kayatar

"Zai jefar da yarinyar ne gaba daya?"

@Makeup With Kimmy tace:

"Ji take kamar, meye na yi ne kam? Ina babata> Kyakkyawar yarinya."

Yadda dan Najeriya ke samar da wuta daga toroso

A wani labarin kuma, wani dan Najeriya ya ba da mamaki yayin da ya bayyana fasaharsa ta samar da bandaki mai samar da wutar girki da ta lantarki.

An ga matashin lokacin da yake tsaka da aikin dasa wannan fasaha tasa, lamarin da ya jawo martanin jama'a a Facebook.

Ba wannan ne karon farko da ake kirkirar abubuwa masu ban mamaki ba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel