Ta Sadu Da Tsohon Saurayi Tana Gab Da Aure, Bayan Wata 9 Ta Haihu, An Rasa Wanene Hakikanin Uban Yaro

Ta Sadu Da Tsohon Saurayi Tana Gab Da Aure, Bayan Wata 9 Ta Haihu, An Rasa Wanene Hakikanin Uban Yaro

  • Wani likita a Najeriya ya bayyana yadda wata mata ta shiga cikin garari sakamakon gwajin DNA
  • Makonni kadan kafin bikinta, ta kwana da tsohon masoyinta, ta samu juna biyu daga baya, kuma ta haihu
  • Wani gwajin kwayoyin halitta da aka yi don sanin ko wanene ainihin uban ɗanta ya nuna cewa duk ba cikin mutanen da ake tunani bane

Wani likitan Najeriya, @drpenking, a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba, ya ba da labarin wata mata da ta yi jima'i da tsohon saurayinta tana gab da aure.

Bayan aure ta fadawa angonta abinda ta aikata kuma ya yafe mata.

Bayan yan makonni sai ta samu ciki.

Wata 9 zuwa 10 bayan yafe mata sai ta haihu, amma sai tsohon saurayin da yayi lalata da matar yace lallai jaririn da aka haifa nasa ne saboda 'dan na kama da shi, legit.ng ta hakkaito.

Kara karanta wannan

Yadda Dangin Mijina Suka Umurci Ɗayansu Ya Gaje Ni Bayan Rasuwarsa, In Ji Matar Yar Jihar Arewacin Najeriya

Gudun mujadala da gardama, ya bukaci ayi gwajin kwayoyin hallita wanda akafi sani da gwajin DNA don gano ainihin mahaifin

A cewar @drpenking, abin ya daurewa mijin kai amma duk da haka ya amince ayi gwajin amma da sharadi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

mata saurayi
An Gano Yayan Matar Da Ta Yaudari Saurayinta Makkoni Kafin Aurensu Ba yayansa Bane
Asali: UGC

A cewar Likitan:

"Wata mata ta sadu da tsohon sauarayinta, makonni kafin tai aure, amma ta yiwa mijin bayani kuma ya yafe mata. Bayan wata 9-10, ta haihu, sai dai tsohon saurayin nata yayi da'awar cewa dan nasa ne, dole ai gwajin kwayoyin halitta dan tabbatar masa da da'awarsa.

"Mijin ya amince ayi, ko dan ya kunyata tsohon saurayin. Sai dai; yace sai tsohon saurayin zai dauki nauyin dawainiyar kudin asibiti kama da ga zirga-zirga da zama a masauki a yankin Lekki har a samu sakamako."

Sakamakon Gwajin Kwayar Mai ban mamaki

@drpenking ya cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

Cika alkawari: Tela ta saka amarya kukan dadi bayan da ta cika alkawari, ta gwangwaje ta

"Sakamako ya fito kuma ya nuna cewa dukkansu biyu ba su da kwayoyin hallitan jaririn."

Hakan na nufin cewa babu Uban yaron cikinsu.

Kallo ya koma sama

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin yan Najeriya:

@rj45cat6_us ya ce:

"Bayan Allah kaji tsoron mata, kai na sake maimaita bayan Allah kuji tsoron mata!"

@mr_wemz ya ce:

"Kafin ka ɗauki jaririnko dawainiyarsa a gida ko saya ka tabbatar an yi gwajin DNA."

@EngrMide ya ce:

"Miji da tsohon...'cai ba sa'a'. kaji tsoro mata ko yaya."

@Bukkiahlawrence ya ce:

"Idan kuma canzawa akai a Haihuwa fa??"

@GiftUzor3 ya ce:

"Dukkan ku kuna cewa"aji tsoron mata "abinda zan fada maka a matsayinka na namiji, ku san irin matar da za ku yi ku zauna da ita a wanan lokaci. amma in kunyi yaudara, kuma za'ai muku haka ka'idar take"

Wata Mata Ta gano mijinta ba Shi Ne Uban Yaronsu Ba

Kara karanta wannan

Za A Fara Ɗaure Mazinata Da Masu Zaman Dadiro A Gidan Yari A Indonesiya

A Wani ci gaban kuma, Legit.ng ta rawaito a baya cewa wata budurwa a kasar Ghana ta na neman amsoshi a yanar gizo bayan samun labarin wani bakon labari daga likitanta, wanda ya shaida mata game da kwayar halittar yaronsu.

A cewar wani mai tasiri a shafukan sada zumunta, David Bondze-Mbir, matar ta nuna cewa ta lura da wasu abubuwa masu ban mamaki a cikin daya daga cikin 'ya'yanta kuma ta yanke shawarar gwada mata Kwayar halittarsa

Sakamakon jarabawar ya fito, sai ya zama cewa yaron nata ne, amma mijinta ba shine uban jaririn ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel