Babu Wata Hujja Da Ke Nuna 'Kafi-zabuwa' Na Da Illa Ga Lafiya, Inji Masana Kimiyyar Abinci

Babu Wata Hujja Da Ke Nuna 'Kafi-zabuwa' Na Da Illa Ga Lafiya, Inji Masana Kimiyyar Abinci

  • Masana kimiyyar abinci sun yi watsi da jita-jitan da aka shafe tsawon lokaci ana yi cewa farin maggi na da illa ga lafiyar jiki
  • Kwararru a bangaren kimiyya sun ce Maggin Ajinomoto bata da illa ko kadan sai dai ma amfani da take da shi a jikin dan Adam
  • Sun ce akwai wani sinadari a cikin kafi-zabuwan wanda ke da matukar alfanu ga kwakwalwa kuma yana rage hawan jini

Masu bincike da masana kimiyyar abinci sun ayyana cewa babu wata hujja a kimiyance da ke nuna cin farin maggin Ajinomoto yana da alaka da rashin lafiya.

Masana kimiyyar wadanda suka bukaci masu cinsa da su yi watsi da jita-jitan da ke yawo game da maggin sun kuma bayyana cewa babu illa tattare da cinsa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Farin Maggi a kwalba
Babu Wata Hujja Da Ke Nuna 'Kafi-zabuwa' Na Da Illa Ga Lafiya, Inji Masana Kimiyyar Abinci Hoto:The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Kafi-zabuwa na da amfani sosai ga lafiyar kwakwalwa

Har ila yau, sun ce kafi-sabuwan na da tarin alfanu ga lafiyar jiki, musamman ma ga kwakwalwa da kuma rage yawan cin gishiri a abinci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun ce babban matsalar da farin maggin ke fuskanta shine kasancewar jabunsa da kayayyaki masu arha a kasuwa amma ba wai batun illa ga lafiya ba.

Da yake jawabi a wani taro da kamfanin Ajinomoto Foods Nigeria Limited, ya shirya, shugaban jami'ar tarayya ta Dutse da ke jihar Jigawa, Farfesa Abdulkarim Mohammad, ya ce sam Maggin bai da illa.

A cewarsa, a wannan zamani da hawan jini yayi yawa, amfani da Ajinomoto na taimakawa wajen rage gishiri a abinci.

Abdulkarim ya ce bata sunan kafi-zabuwan na zuwa ne daga rashin wayar da kan jama'a, rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

FG Tace Gwamnatocin Jihohi ne Suke kara Tsunduma ‘Yan Najeriya Cikin Matsanancin Talauci

An yi bincike kan Ajinomoto a nahiyar Turai da Asiya

A cewarsa, ana samar da maggin ne daga rake, yana mai jaddada cewa sama da kasashen duniya guda 100 na amfani da wannan maggi.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

"Abun da zan iya fadi daga bangarena a matsayina na masanin bincike shine cewa an tsattsauran bincike kan wannan maggi ba wai a Najeriya kawai ba harma a Asiya da Turai saboda takaddamar.
"Abun da masu bincike suka gano shine cewa babu wata alaka tsakanin wannan maggi da kowani rashin lafiya wanda aka ce shine ke haifarwa kamar hawan jini da ciwon zuciya.
"A kimiyyance, idan ka ambaci amino acids, suna da matukar muhimmanci ga jikinmu kuma wannan maggi shi kadai ke cikinsa. Don haka, zan fadi a ko'ina cewa wannan maggi na da inganci."

Ya kara da cewa MSG na da amfani ga lafiyar kwakwalwa kuma ana amfani da shi wajen ayyukan lantarki da dama a jiki.

Kara karanta wannan

"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

Legit.ng ta tuntubi wani magidanci kuma dalibi a bangaren kimiyya da ya nemi a sakaya sunansa inda ya ce shi sam baya son dandanon farin maggi a cikin abinci.

Ya kuma nuna rashin gamsuwarsa da ikirarin da aka yi na cewa bai da illa jiki domin a cewarsa akwai sinadarin ‘Monosodium Glutamate’ kuma yana da illa.

Ya ce:

"Mu maza bamu cika son amfani dashi ba, saboda bai da dadi a baki sannan yana tara miyau. Dama mata ke son saka shi a miya ko abinci, maganar illa kuma bana tunanin a ce ba zai yi ba.
"Masana sun ce sinadarin monosodium Glutamate ka iya jawo cuta ta kiba, yana shafar lafiyar kwakwalwa da kuma shafan lafiyar al'aura; wannan abu ne sananne. Kuma babban abin da ke cikin farin maggi shine Monosodium Glutamate. Ta yaya za a ce bai da illa ga lafiya?"

A nata bangaren wata uwargida mai suna Malama Khadija ta ce tana son amfani da farin maggi musamman wajen hada yaji kasancewar ita ba mutum bace mai son gishiri don tana da lalurar hawan jini.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Aike Da Dalibin Aminu Gidan Kurkuku Bisa Zargin Cin Zarafin Uwar Gidan Buhari

Malama Khadija ta ce:

"Gaskiya ina son farin maggi a girki musamman a wajen hada yaji gashi karamar jaka daya ta isheka girkinka ya dauki dandano a wannan lokaci da kayan sinaran girki suka yi tsada.
"Bana kya taba rabani da farin maggi kuma ina jin dadin dandanonta yanzu kuma da na ji cewa bai da illa kin ga sai na kara kaimi wajen amfani da shi."

Manoman kwai sun kusa hakura da sana'ar a Najeriya

A wani labarin, mun ji cewa manoman kwai sun gaji da yadda farashin abincin kaji ke kara haurawa sama a duk kwanan duniya.

Yawancin masu kiwon kaji masu kwai sun fara hakura suna siyar da kajinsu saboda ba za su iya ci gaba da ciyar da su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel