FG Ta Dorawa Gwamnatocin Jiha Laifin Wurga ‘Yan Najeriya a Talauci

FG Ta Dorawa Gwamnatocin Jiha Laifin Wurga ‘Yan Najeriya a Talauci

  • Gwamnatin Najeriya ta dora laifin hauhawar fatara a Najeriya kan gwamnonin jihohin Najeriya wadanda tace basu hobbasa wurin yaki da talauci
  • Kamar yadda karamin ministan tsari da kasafi na kasa, Clement Agba yace, kashi 72 na talakawan Najeriya sun zama ne a karkar, su kuwa gwamnoni basu duban nan
  • Yace sun fi mayar da hankali wurin gina gadojin sama da filayen jiragen sama wadanda birane kadai suke amfana ba wai talakawan da ya dace a duba ba

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta dora alhakin cigaba da yawaitar talaucin kasmar nan kan gazawar gwamnatocin jihohi wurin bayar da gudumawa a bangaren cigaba tun daga tushe inda ake samun matsalar talaucin, jaridar The Nation ta rahoto.

Baba Buhari
FG Ta Dorawa Gwamnatocin Jiha Laifin Wurga ‘Yan Najeriya a Talauci. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Karamin ministan kasafi da tsari na kasa, Clement Agba ne ya bayyana hakan ga manema labaran gidan gwamnati bayan kammala taron majalisar zartarwar tarayya wanda ya samu shugabancin Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Biya malaman Jami'oi Albashin Nuwamba, Ta Rike Sauran

Channels TV ta rahoto cewa, Agba yana martani ne kan tambayar da aka yi masa kan cewa ko shi da abokiyar aikinsa Zainab Ahmed suna yin wani abu domin rage radadin tsananin rayuwa da yawancin ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Ministan da yayi kokarin yin bayanin cewa yawaitar yunwa da rashi duk ‘yan Najeriya sun saba da shi, yayi bayanin cewa Gwamnatin tarayya tana shirye-shirye masu tarin yawa tana ta kokarin yaye tsananin rayuwa ga jama’a, amma kuma yace gwamnatocin jihohi wadanda a koda yaushe suke samun kaso daga gwamnatin tarayya, sun waskar da kudin zuwa ayyukan da za a ce basu da amfani kai tsaye ga jama’a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa, kashi 72 na talakawan Najeriya suna yankunan karkara ne wanda yace gwamnonin sun yi watsi dasu.

Gwamnoni sun mayar da hankali wurin raya birane, Agba

Kara karanta wannan

Aminu Zai Gurfana Gaban Kotu a Yau Laraba Kan Zargin Cin Mutuncin Aisha Buhari

Ya koka kan yadda gwamnonin jihohin suka mayar da hankali wurin gina gadar sama, filayen jiragen sama da sauran ayyuka da a manyan biranen jihar kadai ake gani a maimakon su mayar da hankali kan habakar rayuwar mazauna karkara.

Agba yace a yayin da jihohi ne ke da mallakin gonakin noma, basu zuba kudi a nan domin a samu sassauci ga mazauna karkara.

Ya shawarci gwamnoni da a maimakon su mayar da hankali wurin gina manyan benaye, gadojin sama da sauransu, zai fi kyau idan suka kirkiro yadda zasu tsamo kama masu yawa daga talauci.

Yan Najeriya 133m ne ke cikin tsananin talauci

A wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar, mutum 133m ne a Najeriya suke cikin tsananin talauci.

NBS din ta bada bayani kan jihohin da suke da kaso mafi yawa na talakawa a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel