Dalibin Nan Aminu Da Aka Tsare Shi Kan Zargin Cin Mutuncin Aisha Buhari Zai Kwana a Gidan Kaso

Dalibin Nan Aminu Da Aka Tsare Shi Kan Zargin Cin Mutuncin Aisha Buhari Zai Kwana a Gidan Kaso

  • Mutane da Kungiyoyin fararen Hula Da dama na kira da a saki aminu ko kuma bashi damar daukan wanda zai tsaya masa wato lauya
  • Kafar sadarwar zamani dai ta bawa mutane da ma gabatar da korafin su ko kuma bukutunsu ga gwamnatocin da suke mulkarsu.
  • Dan Takarar Shugaban kasa na jam'iyyar AAC Omowole Sowore yayi Kira da Uwar gida Buharin Da ta Saki dalibin

Abuja: Wani Rahoto da BBC Hausa ta fitar yau ya nuna cewa an Gabatar da Aminu wannan Dalibin Da ake Zargi Da cin zarafin Uwargida Aisha Buhari Koto.

Rahoto Ya Kuma Nuna da cewa tun a jiya aka gabatar da aminun a gaban wata kotu a Abuja wato 29-ga watan nuwanban wannan watan

Lauyan da ya tsayawa Dalibin Mai Suna CK Agu ya tabbatawa da BBC Hausa Din Cewa

Kara karanta wannan

Aminu Zai Gurfana Gaban Kotu a Yau Laraba Kan Zargin Cin Mutuncin Aisha Buhari

"An gurfanar da wanda ake kara a gaban kotun a babban birnin Tarayya Abuja, Amma bai amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ba ko aikatawa ba"
'An Nemi a bada belin Aminu tun a ranar 25-ga wannan watan da muke ciki amma abun ya ci tiara wanda har zuwa yanzun nan da muke magana" inji lauyan Aminu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun nemi kotu da ta bada Aminu beli bisa dalilin rashin lafiya da kuma cewa shi aminun zai fara jarabawa a makarantarsu a cikin watan gobe "

Rahotan yace an nemi a bada shi belin a zaman jiyan, amma kotu taki ta kuma umarci yan sanda da su cigaba da tsare shi.

Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai yace '' yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari bukatar bada shi beli.''

Kara karanta wannan

Jami'anj Tsaro Sun ki Su Bayyana Ko A Wanne Hali Aminu Yake Ciki Baya Da Ya Shafe Mako Guda A Hannunsu

Tsare Aminu Muhammad wanda dalibi ne a jami'ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya tayar da kura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

har yanzu dai mutane na tofa albarkacin bakinsu kan batun yayin da wwasu ke yabo wasu kuma sukan mataki da uwar gidan Buharin ta dauka akan Amunun, inda aka bayyanashi da cin zali ko kuma azabtarwa kamar yadda wasu suka bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel