Dalilin Watsi da Dokar Haramtawa K/Napep Amfani da Manyan Tituna Bayan Kwana 1

Dalilin Watsi da Dokar Haramtawa K/Napep Amfani da Manyan Tituna Bayan Kwana 1

  • Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta nemi ta hana masu Keke Napep amfani da manyan titunan jihar Kano
  • Kwatsam sai ga sabuwar sanarwa cewa gwamnatin jihar Kano ta janye wannan hukunci sai zuwa nan gaba
  • Ana zargin cewa hangen siyasa ya dumfaro, shiyasa Gwamnatin Kano tayi gaggawar janye wannan tsari

Kano - Kafin a je ko ina, sai aka ji gwamnatin jihar Kano ta dakatar da umarnin da ta ba direbobin Keke Napep na amfani da duk wasu manyan tituna.

Sahelian Times tayi bincike, inda ta gano wannan mataki da aka dauka bai rasa nasaba da zaben da hukumar INEC za ta shirya nan da watanni uku.

Hukumar KAROTA tace an tanadi manyan motoci 100 da kananan motocin haya 50 da za a rika amfani da su a titunan da aka haramtawa Keke Napep.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Amma da mutane suka taso gwamnati a gaba da suka, dole aka yi watsi da wannan sabuwar doka.

An canza shawara da gaggawa

A ranar da dokar ta soma aiki, Legit.ng Hausa ta fahimci mutane da-dama sun koma yawo a kafa domin babu isassun abubuwan hawan da za su hau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lura da haka, gwamnatin Kano tayi maza sake nazari, la’akari da cewa hakan zai iya jawo jam’iyyar APC da ke neman sake lashe zabe ta ta sha kasa.

Keke Napep
Keke Napep a Kano Hoto: Ibrahim Aminu Dandago
Asali: Facebook

Akwai siyasa a lamarin?

Direbobin Keke Napep suna da matukar yawa a jihar Kano, kuma za su iya kauracewa jam’iyyar APC mai mulki a 2023 saboda tsarin da aka kawo.

A wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta saurara, an ji Mataimakin Gwamna Nasiru Yusuf Gawuna yana bayanin cewa sun saurari koken jama’a a kan dokar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: FG Ta Wajabta Fara Koyar Da Daliban Firamare Da Harsunan Hausa, Yarbanci Da Igbo A Makarantun Najeriya

Nasiru Gawuna wanda shi ne ‘dan takarar Gwamnan Kano a zaben 2023, ya yi alkwari gwamnati za ta zauna domin sake duba matakin da ta dauka jiya.

An ji Gawuna mai fuskantar barazana daga jam’iyyun hamayya irinsu NNPP, ADC da PDP a zaben Gwamna yana cewa ai saboda jama’a gwamnati take aiki.

Jim kadan bayan haka sai aka ji shugaban KAROTA, Hon Baffa Babba Dan’agundi, a bidiyo yana cewa an janye dokar zuwa wani lokaci, amma za ta dawo.

Amma ‘yan siyasa irinsu Salisu Yahaya Hotoro suna ganin cewa wannan mataki ya nakasa jam’iyyar APC tuni, hakan zai jawo masa bakin jini a filin zabe.

An yi amai an lashe

Rahoton da muka samu daga jihar Kano tun a jiya ya bayyana cewa, gwamnati ta janye dokar da ta kawo na haramta bin wasu tituna ga 'Yan Keke Napep.

An ji labari cewa daga cikin titunan da aka nemi a hana bi akwai na Ahmadu Bello Way ta titin Mundubawa zuwa Gezawa da titin Tal’udu a hanyar Gwarzo.

Kara karanta wannan

"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

Asali: Legit.ng

Online view pixel