A Karshe Gwamnatin Tarayya Tayi Magana Game da Kara Farashin Fetur Zuwa N400

A Karshe Gwamnatin Tarayya Tayi Magana Game da Kara Farashin Fetur Zuwa N400

  • Sanarwar da ta fito daga bakin hukumar NMDPRA ta nuna gwamnati ba za ta kara farashin fetur ba
  • NMDPRA tace farashi na nan a yadda aka sani, kuma mutane su daina sayen mai, suyi ta boyewa
  • Gwamnati tace an tanadi wadataccen fetur da ake bukata a Najeriya yayin da aka zo karshen shekara

Abuja - A ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba 2022, Gwamnatin tarayya ta musanya maganar da ake yi na cewa farashin man fetur zai tashi.

A wani jawabi da ya fito daga bakin hukumar NMDPRA mai kula da harkar fetur, Vanguard ta tabbatar da kudin litar fetur ba zai canza ba.

Duk da wahalar fetur da ake yi a jihohin kasar nan, hukumar NMDPRA ta dage cewa akwai isasshen mai da za iya kwanaki 34 mutane na sha.

Kara karanta wannan

Daga karshe, za a fara koyar da dalibai da harshen Hausa a makarantun firamare

Hukumar tace Najeriya tana da fetur a ajiye, duk da cewa akasin haka mutane suke gani a gidajen mai da wajen masu yin harkar bumburutu.

Akwai fetur har Junairu

Sanarwar NMDPRA ta fadakar da mutane cewa ba za a kara kudi ba, kuma kamfanin NNPCL ya shigo da fetur da za a iya sha har farkon 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An yi kira ga ‘yan kasuwa da sauran al’umma da su guji sayen fetur domin su adana, kuma su daina boye man fetur da nufin su saida da tsada.

Motoci
Motoci a hanya Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Watan Disamba ya iso

Kamar yadda dokar PIA tayi tanadi, hukumar tarayyar ta bayyana cewa za ta cigaba da sa ido a kan yadda ake raba mai a karshen shekara nan.

A daidai wannan lokaci, ana amfani da fetur sosai saboda zirga-zirga da bukukuwan kirismeti da na shiga sabuwar shekara da ake yi a Disamba.

Kara karanta wannan

Dalilin Watsi da Dokar Haramtawa K/Napep Amfani da Manyan Tituna Bayan Kwana 1

Mazauna garuruwan Abuja da Legas sun tabbatar da cewa lamarin wahalar mai ya karu a ‘yan kwanakin nan, ana saida lita daya a kan N260.

A wasu garuruwan, ko da mutum zai saye fetur a gidajen man da suka yi watsi da farashin gwamnati ne, sai ya yi ta fama da bin dogon layi.

A wajen ‘yan bunburutu, Vanguard tace sai mutum ya tanadi N350 sannan zai saye lita guda.

Kasafin kudin 2023

Rahoto ya zo cewa Ministar kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin ta fadawa Majalisar wakilan tarayya dalilin ganin karin N1.7tr a kasafin kudin 2023.

Zainab Ahmed tayi karin haske a kan abin da ya shigar da N206,242,395,000 a kasafin kudin ma’aikatar jin kai da bada tallafi ba tare da sanin Minista ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel