Ministan Ilimi Yace Za'akashewa Jami'ar Usman Dan Fodio Naira Biliyan 3.26

Ministan Ilimi Yace Za'akashewa Jami'ar Usman Dan Fodio Naira Biliyan 3.26

  • Jami'oin Gwamnatin Tarayya Dai Na Fusaktan Nakasu da koma Baya wajen gudanar da jami'oinsu kamar yadda Kungiyar ASUU tai ikirari
  • Jami'ar Usman Dan Fodio na Cikin tsoffi kuma manyan jami'on Kasar nan da suke yaye manya da mashahuran mutane
  • Har Yanzu Kungiyar ASUU na kuka da gwamnatin Tarayya kan abubuwan da gwamnatin taki cika mata na alkawuran data dauka

Abuja: Ministan Ilimi Adamu Adamu ya ce an bayar da kwangilar Zagaye Jami'ar Usman Dan Fodio ga kamfanin Amis Construction Nigeria Limited.

An amince da bada kwanligilar ne a zaman da majalissar koli da aka gabatar a jiya Laraba kamar yadda Daily Trust ta rawaito

Kwangilar dai ana tunanin zata lakume kudi kimanin naira Dubu Miliyan Uku da Doriya kamar yadda Ministan ya sanar.

Ya ce hukumar Ilimin tarayya ta kuma amince da Naira 5,107,364,373.62 domin buga takardun jarabawar kamala Sakandire ta kasa (NECO).

Kara karanta wannan

Tashin Hankali, Bayan Yayi Tatil da Giya, Kofur Ya Buge Babban Janar Da Mota Har Lahira

Adamu
Gwamnatin Tarayya Zata Zagaye Jami'ar Usman Dan Fodio Kan Kudi Naira Biliyan 3.26 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adamu yace:

"An bada kwangilar ne a ga ‘yan kwangila takwas, domin yin aikin"

Adamu ya ce majalisar kolin hukumar ilimin ta kuma amince da kwangilar samar da motocin daukar marasa lafiya 18 a makarantun sikandiren Hadaka a fadin kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce an amince da N2,578,948,164.36 don siyan motocin aiki guda 145 ga hukumar kiyaye haddura ta kasa.

"Kamfanin Dangote Peugeot ne za su samar a cikin kwanaki 30; yayin da kamfanin Mikaino International su ma zasu samar a cikin kwanaki 14. Kuma an bada gudunmawar jigilar Landtrek guda 18 akan N18,172,875.00 yayin da kowanne ya kai N145,383,000.00 da kuma wasu jigilar motoci 90 akan kudi N20,889,999 wanda a jimlance yakai N1,880,099,910.00".
"kamfanin Mikaino, zai samar da motocin daga kamfanin Nissan Almera Acenta (20) akan N12,255,000.00 kowacce.”

Kara karanta wannan

2023: Shugaba Buhari ya fadi babban abin da zai yi kafin ya sauka a mulki

Ba Za a Biya Ku Albashin Aikin Da Baku Yi Ba – FG Ga Malaman ASUU

Gwamnatin tarayya ta jadadda cewa ba za a biya malaman jami’a albashin aikin da basu yi ba kamar yadda yake a tsarin ‘babu aiki babu biya’ Daily Trust ta rahoto.

Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana haka yayin da yake martani ga zanga-zangar kungiyar ASUU kan yanayin biyan da aka yi masu a watan Oktoba.

Sai dai kuma, mambobin kungiyar sun samu rabin albashi a karshen watan Oktoba, lamarin da bai yiwa malaman jami’ar dadi ba.

A ranar Laraba, manema labarai na fadar shugaban kasa sun zanta da ministan bayan taron majalisar zartarwa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Villa, Abuja.

Da yake martani, Adamu ya ce matsayin gwamnatin tarayya shine ne ba za a biya Lakcarorin albashin aikin da basu yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel