Babbar Magana: An Gano Fatattun Mutane 100 Masu Hatsari Dake Daukar Nauyin 'Yan Ta'adda

Babbar Magana: An Gano Fatattun Mutane 100 Masu Hatsari Dake Daukar Nauyin 'Yan Ta'adda

  • Gwamnatin tarayya tace ta ƙara gano manyan mutane 100 masu haɗari dake tura wa kungiyar Boko Haram kuɗi
  • A wurin taron ministoci kan yaki da ta'addanci, Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, yace watanni 18 aka shafe ana bincike
  • Yace tuni gwamnati ta kama wasu kuma ta fara bin matakan doka domin su girbi abinda suka shuka

Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, yace gwamnatin tarayya ta ƙara gano manyan mutane 100 masu hatsari da ake zargin suna ɗaukar nauyin ƙungiyar Boko Haram.

Yace waɗannan mutanen da aka gano suna da alaƙa da ƙasashe 10 mabanbanta a Duniya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola.
Babbar Magana: An Gano Fatattun Mutane 100 Masu Hatsari Dake Daukar Nauyin 'Yan Ta'adda Hoto: Rauf Aregbesola
Asali: Twitter

Aregbesola ya faɗi haka ne a wurin taron Ministoci karo na uku da aka gudanar kwanan nan a ƙasar Indiya kan yaki da ta'addanci mai taken, "Ba kuɗi ga ɗan ta'adda."

Kara karanta wannan

'Ba Tausayi' Kotu Ta Yanke Wa Mutumin da Aka Kama da Katin Zabe Sama da 100 Hukunci a Sokoto

A wata sanarwa da hadimin ministan, Abdulmalik Suleiman, ya raba wa manema labarai ranar Lahadi, Aregbesola ya faɗi wasu alfanun sashin tattara bayanan sirri na kuɗaɗe (NFIU) a yaƙi da ta'addanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa yace:

"NFIU ta taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ɓangaren tattara bayanai, tsaro da ayyukan rundunar soji. Babban aikin NFIU shi ne haɗa kai da takwarorinta na wasu nahiyoyi a duniya."
"A 2019, NFIU ta buɗe shafin bincike mai zurfi kan masu angiza wa mayaƙan Boko Haram kuɗaɗe. Wannan binciken da ya shafe watanni 18 kafin kammala shi ya gano masu hannu 100."
"Binciken ya bankaɗo mutane 100 masu matuƙar hatsari da ake zargin suna taimaka wa ta'addanci da kuɗaɗe kuma an gano suna da alaƙa da ƙasashe 10."
"Bugu da kari sakamakon binciken ya taimaka har mutum 48 daga ciki suka shiga hannu kuma ana ci gaba da bin matakan hukunta su."

Kara karanta wannan

2023: Atiku da Tinubu Sun Kara Shiri, Sun Yi Sabbin Naɗe-Naɗe a Kwamitin Yakin Neman Zabe

Bayan haka ministan ya yi kira da a ƙara inganta walwala da jin daɗin 'yan Najeriya mazauna, ɗalibai da masu neman aiki a ƙasar Indiya.

Gwamnatin Buhari Ta Gama Binciken Gano Masu Hannu a FashinɓGidan Yarin Abuja

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya tace ta kammala bincike kan fashin gidan gyaran halin kuje dake Abuja

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa gwamnati ba zata fito da sakamakon binciken ba saboda abu ne da ya shafi tsaron al'umma.

Yace gwamnati mai ci karkashin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta yi abun a yaba a yaki da Boko Haram domin zuwanta ne aka kwato garuruwa da yan ta'adda suka kwace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel