Bola Tinubu da Atiku Abubakar Sun Yi Sabbin Nade-Nade a Kwamitin Yakin Neman Zabe 2023

Bola Tinubu da Atiku Abubakar Sun Yi Sabbin Nade-Nade a Kwamitin Yakin Neman Zabe 2023

  • Manyan 'yan takarar shugaban ƙasa biyu na sahun gaba sun yi sabbin naɗe-naɗe a tawagar yakin neman zaɓensu na 2023
  • Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya naɗa mai taimaka masa musamman yayin da Tinubu na APC ya nada kakakin kwamitin arewa ta yamma
  • A cewar sanarwan naɗin guda biyu, waɗanda aka baiwa mukaman zasu kama aiki ne nan take ba ɓata lokaci

Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya naɗa Mista Nath Yaduma, a matsayin mai taimaka masa na musamman a ɓangaren sadarwa.

Atiku, a wata sanarwa da kakakinsa, Paul Ibe, ya fitar ranar Laraba a Abuja, yace naɗin zai kama aiki ne nan take, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Yan takarar shugaban kasa.
Bola Tinubu da Atiku Abubakar Sun Yi Sabbin Nade-Nade a Kwamitin Yakin Neman Zabe 2023 Hoto: Atiku Abubakar, Bola Tinubu
Asali: Twitter

Kafin yanzu da ya samu wannan muƙami a tawagar kamfen PDP, Mista Yaduma, haifaffen jihar Adamawa, ya jima a matsayin hadimin Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa, Na Hannun Daman Atiku Ya Maida Masa Martani

Haka nan kuma ya rike mukamai daban-daban ciki har da mai ba da shawari na musamman kan ayyuka na musamman a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Obasanjo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaduma ya yi karatu a Makarantar Inshora, Institute of Insurance, Kent, birnin Landan da kuma City College da ke New York ta ƙasar Amurka.

Wane naɗi Bola Tinubu ya yi?

A ɗaya bangaren kuma, kwamitin kamfen Tinubu/Shettima ya naɗa Amas Anka, shugaban Talabijin ɗin Thunder Blowers a matsayin mai magana da yawun tawagar arewa ta yamma.

Tsohon ma'aikacin gidan Talabijin na gwamnatin Najeriya (NTA), Mista Anka ya samu labarin naɗinsa ne a wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Gwamna Bello Matawalle, Ko'odinetan kwamitin kamfen Tinubu/Shettima na arewa ta yamma ne ya sanar da naɗin a taron tawagar wanda ya gudana a Kaduna.

Kara karanta wannan

Wike Zai Koma Bayan Tinubu? Gaskiya Ta Fito Yayin da Gwamnan APC Ya Faɗi Wata Bukata

Bugu da ƙari, a wata sanarwa da Mista Anka ya fitar ranar Laraba, yace wannan naɗin wanda ya fara aiki nan take ya maida shi matsayin mashawarci na musamman ga Kodinetan arewa ta yamma.

A cewarsa, naɗin na ɗaya daga cikin dabaru da shirye-shirye kaddamar da fara harkokin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa a shiyyar.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa Anka, malami ne a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau. Ya yi digiri na uku a fannin kimiyyar siyasa.

A wani labarin kuma gwamnonin kudu maso kudu na PDP sun kara zama a Bayelsa, sun yanke mara wa Atiku/Okowa baya a 2023

Duk da ba'a hangi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a wurin ba, gwamnonin sun ce ba zasu watsa wa jam'iyyarsu ta PDP ƙasa a ido ba a zaɓe mai zuwa.

Waɗaɓda suka halarci taron sun haɗa da Godwin Obaseki na Edo, Duoye Diri na Bayelsa, Ifeanyi Okowa na Delta da kuma Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Abubakar Na Shirin Janyewa Daga Takarara Shugaban Ƙasa? Gaskiya Ta Fito

Asali: Legit.ng

Online view pixel