Kotu Ta Daure Mutumin da Aka Kama da Katin Sabe 101 Shekara 1 a Gidan Yari

Kotu Ta Daure Mutumin da Aka Kama da Katin Sabe 101 Shekara 1 a Gidan Yari

  • Kotun Majistire a jihar Sakkwato ta yanke wa Nasiru Idris da aka kama da katin zaɓe 101 hukuncin zaman gidan Yari na shekara ɗaya
  • A wata sanarwa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar ranar Lahadi tace ana cigaba da shari'ar wanda aka kama a Kano
  • INEC tace zata shirya taro a jihar Legas bayan haka zata sanar da wuraren da mutane zasu je karban katin zaɓensu a faɗin ƙasar nan

Sokoto - Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) tace mutumin da aka kama da Katin zaɓe 101 a Sakkwato, Nasiru Idris, Kotu ta yanke masa hukuncin zaman gida gyaran Hali na shekara ɗaya.

The Caɓle ta ruwaito cewa INEC ta sanar da hukunta mutumin ne a wata sanarwa da Festus Okoye, kwamishinan hukumar na ƙasa ya fitar ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

2023: Kotun Daukaka Kara Ta Kwace Tikitin Ɗan Takarar PDP a Kano, Ta Baiwa Mace

Katin PVC.
Kotu Ta Daure Mutumin da Aka Kama da Katin Sabe 101 Shekara 1 a Gidan Yari Hoto: thecable
Asali: UGC

Idan baku manta ba Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa a ranar 10 ga watan Oktoba, 2022 'yan sanda suka cafke Idris bayan samun wasu bayanan sirri.

Sanarwan INEC tace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A wasu makonni da suka gabata, hukumar yan sanda ta kama wasu mutane bisa zargin mallakar Katunan zaɓe ba kan ƙa'ida ba a wasu jihohi."
"A ɗaya daga cikin Kes ɗin, yan sanda sun miƙa binciken da suka yi ga hukumar zaɓe, sakamakon haka Kotun Majistire a Sakkwato ta hukunta Nasiru Idris bayan kama shi da katin zaɓe 101. An yanke masa shekara ɗaya a gidan Yari."
"Haka nan yan sanda a Kano sun kama wani mutumi ɗauke da Katunan zaɓe 367. Tuni aka garfanar da wanda ake zargin gaban Ƙuliya kuma INEC na bibiyar shari'ar."

Game da batun karban katin PVC, INEC tace zata zauna da baki ɗaya kwamishinonita na jihohi a jihar Legas daga ranar 28 ga watan Nuwamba zuwa ranar 3 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Na Ɗirka Wa Budurwata Ciki da Izinin Mahaifiyarta, Matashi Sadiq Ya Yi Wa Kotu Bayani Dalla-Dalla

Bayan kammalawa ne hukumar tace zata sanarwa yan Najeriya ranakun da zasu garzaya su karɓi Katin zaɓensu a dukkan sassan ƙasar nan, Punch ta ruwaito.

Kotun Daukaka Kara Ta Maida Dan Takarar Gwamnan Taraba Na APC

A wani labarin kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da sahihancin ɗan takarar gwamnan jihar Taraba a inuwar jam'iyyar APC

Kafin wannna Hukunci, babbar Kotun tarayya mai zama a Jalingo, babban birnin jihar ta rushe zaben fidda gwanin APC da ya samar da Sanata Bwacha a matsayin ɗan takarar gwamna.

Sakamakon haka APC ta ɗaukaka kara zuwa gaba, inda Kotun Mai zama a Yola ta jingine hukuncin baya, kana da maida wa Bwacha takararsa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel