Gwamnatin Buhari Ta Gama Binciken Gano Masu Hannu a Fashin Gidan Yarin Abuja

Gwamnatin Buhari Ta Gama Binciken Gano Masu Hannu a Fashin Gidan Yarin Abuja

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala bincike kan yadda 'yan ta'adda suka fasa gidan Yarin Kuje a Abuja
  • Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, yace gwamnatin Buhari zata bar abin a zo a gani a ɓangaren yaƙi da Boko Haram
  • Ya kuma ba da tabbacin cewa sun shawo kan tsaikon da ake samu wajen yin Fasfo

Abuja - Gwamnatin tarayya ta kammala bincike kan fashin gidan gyaran halin Kuje, wanda mayaƙan Boko Haram suka yi a ranar 5 ga watan Yuli, 2022.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana haka ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja.

Fashin gidan yarin Kuje.
Gwamnatin Buhari Ta Gama Binciken Gano Masu Hannu a Fashin Gidan Yarin Abuja Hoto: Bashir Ahmad
Asali: UGC

Sai dai ya bayyana cewa sakamakon binciken abu ne da ya shafi tsaro wanda gwamnati ba zata iya bayyana wa duniya ba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ministan yace wasu daga cikin Fursunonin da suka tsere yayin harin 'yan ta'addan sun sake shiga hannu yayin da da yawa ake ci gaba da nemansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasa gidan yarin da ƙungiyar ta'addancin ta yi ya haddasa tserewar Fursunoni sama da 600, ciki har da mayaƙanta.

Da yake hira da manema labarai a Abuja yayin bayyana ayyukan ma'aikatarsa, Ministan yace babban aikin da gwamnatin Buhari zata bari shi ne kwato yankunan da Boko Haram ta kwace iko da su a baya.

Aregbesola yace:

"A 2015 Boko Haram ta kwace iko da wasu yankuna a ƙananan hukumomin Adamawa, Yobe da Borno amma a yanzun an samu nasarar fatattakarsu."
"Eh tabbas har yanzun akwai ƙalubale nan da can amma ku sani babu ƙasar dake zaune babu wani kalubale ko ɗaya a gabanta."

Mun shawo kan tsaikon samun Fasfo - Aregbesola

Ministan ya ƙara da tabbatarwa 'yan Najeriya cewa duk wasu kalubale dake kawo tsaiko wajen samun Fasfo an warware su.

Mista Aregbesola ya amince da cewa matakan da ake bi wajen ɗaukar bayanai ne suka jawo tsaikon da ake samu kuma an ɗauki matakan magance su.

A wani labarin kuma Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai gabatar da sabbin takardun kuɗi a Gobe Laraba

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, yace a ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba, 2022, shugaban ƙasa Buhari zai bayyana kalar sabon kudin Naira.

Ya kuma jaddada cewa kuɗaɗen zasu fara shiga hannun jama'a daga ranar 15 ga watan Disamba, 2022 kuma za'a daina karban na yanzu a karshen watan Janairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel