Abubuwa 5 Da Kowane Dan Najeriya Ya Kamata Ya Sani Game Da Sabbin Takardun Naira Na CBN Kafin Su Shigo Gari

Abubuwa 5 Da Kowane Dan Najeriya Ya Kamata Ya Sani Game Da Sabbin Takardun Naira Na CBN Kafin Su Shigo Gari

  • CBN na cigaba da wayar da kan da ilimantar da yan Najeriya kan sauya fasalin takardan Naira
  • Akwai bayanai biyar da CBN ke son yan Najeriya su sani kafin a saki sabuwar takardar naira kasa da wata guda
  • CBN ta sanar da sauya fasalin Nairan a watan Oktoba don dawo da takardun naira da ke hannun mutane zuwa banki

Babban bankin Najeriya, CBN, na cigaba da kokarinta na ganin yan Najeriya sun shirya tarbar sabbin takardun naira.

Ana sa ran sabbin takardun nairan za su fara shiga hannun mutane daga ranar Alhamis, 15 ga watan Disamban 2022.

Emefiele
Abubuwa 5 Da Kowane Dan Najeriya Ya Kamata Ya Sani Game Da Sabbin Takardun Naira Na CBN Kafin Su Shigo Gari. Hoto: CBN
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta rahoto Shugaba Muhammadu Buhari ya bada goyon bayansa ga sauya nairan kuma yana son yan Najeriya su bada hadin kai.

Kara karanta wannan

Waiwayen Tarihi: Lokuta 11 Da Aka Yiwa Kudin Najeriya Sauye-Sauye Daga 1960

A cewar Buhari, kasar za ta amfana sosai da sabon tsarin, musamman tasirin da zai yi kan kudaden haram da aka boye.

Abubuwa Biyar Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Sauya Fasalin Takardun Naira

1. Sauyin ya shafi manyan takardun kudi ne kawai.

A jawabinsa game da sabbin takardun naira, Godwin Emefiele, gwamnan CBN, ya ce canjin kawai zai shafi manyan kudi ne da suka hada da N200, N500 da N1,000.

2. Ranar da tsohon takardar naira zai dena aiki

A cewar CBN, sabbin takardun nairan za su fito daga ranar 15 ga watan Disamban 2022, amma za a cigaba da amfani da tsaffin nairan har zuwa ranar 31 ga watan Janairu, daga nan za a dena amsarsu.

3. Kai kudi banki

Emefiele, a jawabinsa ya ce duk wanda ke da tsohon takardar N200, N500, da N1,000 ya zama dole ya kai banki.

Kara karanta wannan

N165bn sun dawo: CBN ya ce sabon kudi ya fara yawo, sabon batu mai muhimmanci ya fito

Kalamansa:

"Ana shawartar kwastomomin bankuna su fara zuwa bankuna su kai tsaffin nairari domin su karbi sabbin da zarar an sake su a tsakiyar Disambar 2022."

4. An dakatar da karbar harajin saka kudi a banki

Domin saukaka wa, CBN ta kuma sanar da cewa za ta dakatar da karbar harajin da ake biya yayin saka kudi a asusun banki.

CBN ta kuma kara da cewa ta cire kayyade adadin kudin da yan Najeriya za su iya saka wa a asusunsu.

Sanarwar na CBN ta ce:

"Saboda sauyi daga tsoho zuwa sabbin nairari, an dakatar da karbar harajin da banki ke karba don saka kudi a asusu nan take.
"Don haka, DMBs su sani kada a caji kwastoma don kawo kudi cikin asusun ajiyarsu."

5. Tsawaita awannin aiki

Ana sa ran bankuna su tsawaita adadin kwanakin aikinsu a sati domin bawa mutane damar zuwa su kai kudinsu banki.

Kara karanta wannan

Bayan Sauyin Launi, Buhari Ya Nuna Inda Sababbin Kudin da Aka Yi Suka Bambanta

CBN ta umurci dukkan bankuna su kasance a bude daga Litinin zuwa Asabar don bawa kwastoma damar kawo kudi banki.

Legit.ng ta nuna kwafin sanarwar sabon canjin lokacin aikin bankunan a wani rahoto a baya.

Abin da yasa CBN za ta sauya fasalin wasu takardun Naira a Najeriya

A wani yunkuri na yaki da ta'addanci da boye kudade da kuma yaki da kudaden jabu, CBN ya ce zai fara rarraba sabbin takardun N100, N200, N500 da N1000 daga ranar 15 ga Disamba.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa inda ya ce za a sake fasalin Naira ne bayan samun amincewa daga Shugaba Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel