CBN Ya Fara Rarraba Sabbin Kudi, Yace an Mayar da Tsofaffin Kudi N165bn Zuwa Banki

CBN Ya Fara Rarraba Sabbin Kudi, Yace an Mayar da Tsofaffin Kudi N165bn Zuwa Banki

  • Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce akalla N165bn ne na tsofaffin kudi jama'ar kasar nan suka mayar bankuna yayin da aka fara kashe sabbin kudi
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da CBN ya sanya wa'adin daina amfani da wasu nau'ikan kudade a kasar nan saboda kirkirar sabbi
  • Akalla akwai kudaden da suka kai N2.7tr a hannun 'yan Najeriya da ko dai suka boye ko kuma ake juya su tsakanin jama'a

FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa, sabbin kudaden da shugaba Buhari ya kaddamar sun fara yawo a Najeriya tun daga ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba.

Babban bankin ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yanzu an mayar da N165bn na tsofaffin kudade zuwa banki tun bayan sanar da wa'adin daina karbar wasu nau'ikan kudin kasar nan, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Bayyana Muhimman Dalilan da Suka da Ya Sake Fasalin Takardun Naira

Bayan wata tattaunawa game da tsarukan kudi da aka yi a Abuja a jiya Laraba, daraktan kudi na CBN, Rasheed Adam ya bayyana cewa, an mayar da kudaden fiye da yadda ake tsammani.

CBN ya fadi adadin kudaden da aka dawo dasu banki
CBN Ya Fara Rarraba Sabbin Kudi, Yace an Mayar da Tsofaffin Kudi N165bn Zuwa Banki | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Manufar sake fasalin Naira

Babban bankin ya bayyana cewa, manufar sake fasalin kudin ba komai bane face hanyar iya kula da zagayawar kudi a tsakanin 'yan kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adadin da Adam ya bayyana ya zarce abin da bankin CBN ke tsammanin karba daga 'yan Najeriya a kowane wata bayan sanar da sake fasalin, NairaMetrics ta ruwaito.

Adam ya bayyana cewa, dandazon 'yan Najeriya ne suka zo domin mayar da kudadensu banki, inda yace CBN ba zai kara wa'adin da aka shar'anta ba na 31 ga watan Janairun badi.

A cewar rahotanni, CBN ya ce akwai akalla 2.7tr a hannun jama'a a madadin bankunan kasar nan.

Kara karanta wannan

Kowa Ya Kai Tsaffin Kudinsa Banki, Ba Zamu Kara Wa'adin Ko Minti Daya Ba: CBN

'Yan Najeriya sun shiga mamaki da cece-kuce bayan da babban bankin ya nuna kudaden da aka sauya wa fasali.

Yadda batun sake fasalin kudi ya faro

Idan baku manta ba, babban bankin Najeriya ya sanar da aniyarsa ta sake fasalin kudin kasar nan, kuma hakan ya samu amincewar shugaba Buhari.

'Yan Najeriya sun kagu da sanin yadda sauyin zai zama, lamarin da yasa ake ta yada jita-jita da cece-kuce a kasar.

Majalisar dattawa ma ta amince da sauyin, kuma tuni aka shirya har aka kaddamar dashi a iya Laraba 23 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel