Dalilin Da Yasa CBN Zata Sauya Wasu Takardun Kudaden Najeriya

Dalilin Da Yasa CBN Zata Sauya Wasu Takardun Kudaden Najeriya

  • Babban bankin Najeriya, CBN, ya bayya acewa matakin dakatar da ta'addanci, boye kudi da yaki da jabun Naira suna cikin dalilan sauya wasu takardun
  • An gano cewa, ya dace a dinga sauya fasalin kudin kasa cikin shekaru 5 zuwa 8 amma wannan ne karo na farko da za a sauya cikin shekaru 20
  • Wasu masu kiyasn sun hango kalubalen tattalin arziki kan wannan matakin, yayin da wasu suka ce babu abinda zai faru sai cigaba da za a samu

FCT, Abuja - A wani yunkuri da ta sanar matsayin mataki na yaki da ayyukan ta’addanci, boye kudade da kuma yaki da kudin jabu, babban bankin Najeriya (CBN) ya ce zai fara rarraba sabbin takardun N100, N200, N500 da kuma takardar N1000 daga ranar 15 ga Disamba.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da za su iya faruwa idan CBN ya buga sababbin N200, N500 da N1000

Gwamnan babban bankin kasa, CBN, Godwin Emefiele, wanda ya bayyana hakan a jiya yayin wani taron tattaunawa na musamman ya ce za a sake fasalin kudin Naira ne bayan amincewar gwamnatin tarayya, Daily Trust ta rahoto hakan.

CBN Emefiele
Dalilin Da Yasa CBN Zata Sauya Wasu Takardun Kudaden Najeriya. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

An gano cewa, duk da cewa mafi kyawun abin da ya fi dacewa a duniya shi ne manyan bankunasu sake tsarawa, samarwa da rarraba sababbin takardun kudin cikin gida a kowacce shekara 5-8, Naira ba a sake fasalin ba a cikin shekaru 20 da suka wuce.

Sai dai wasu masu lura da al’amura sun banbanta kan yiwuwar sake fasalin Naira inda wasu ke cewa zai yi tasiri ga tattalin arzikin kasar yayin da wasu ke cewa babu abin da zai sauya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Babban Bankin Najeriya Ya Bayyana Dalilin Hakan

A cewar Emefiele:

"A cikin 'yan kwanakin nan, sarrafa kudaden yan fuskantar kalubale mai yawa wanda hakan yasa ba a ganin nagartar babban bankin da kasar baki daya.

Kara karanta wannan

Bana Bukatar Matar Aure Tunda Na Iya Girki Da Goge-goge: Matashi Dan Shekaru 47 Ya Ki Aure

"Ana yawan boye kudaden inda alkaluma suka nuna cewa sama da kashi 85 cikin 100 na kudaden da ke zagayawa basu cikin ma'adanar bankunan kasuwanci."

Ya kara da cewa:

“A bayyane yake, kudaden da ake rarrabawa sun ninka fiye da ninki biyu tun daga shekarar 2015, inda suka tashi daga Naira tiriliyan 1.46 a watan Disambar 2015 zuwa Naira tiriliyan 3.23 kamar yadda aka gano a watan Satumbar 2022."

Ya bayyana cewa CBN na da yakinin cewa al’amuran ta’addanci da garkuwa da mutane za su ragu domin samun makudan kudade a wajen bankunan da ake amfani da su wajen samun kudin fansa za su fara raguwa

CBN Zata Sake Tsarin Wasu Takardun Kudin Najeriya

A wani labari na daban, Babban bankin Najeriya a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoban 2022 ya bayyana cewa zai sauya tsarin wasu kudin Najeriya.

Gwamnan babban bankin Najeriyan, Godwin Emefiele ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Abuja, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: CBN Zata Sake Tsarin Wasu Takardun Kudin Najeriya

Babban bankin Najeriyan yace zai sauya tsarin N200, N500 da N1000 kuma sabbin kudaden zasu fita daga ranar 15 ga watan Disamban 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel