Bayan Sauyin Launi, Buhari Ya Nuna Inda Sababbin Kudin da Aka Yi Suka Bambanta

Bayan Sauyin Launi, Buhari Ya Nuna Inda Sababbin Kudin da Aka Yi Suka Bambanta

  • Muhammadu Buhari yayi bayanin abin da ya sa ya amince a canza manyan takardun kudi
  • Shugaban kasar yace rabon da a canza kudi shekaru 20 kenan, don haka takardun Nairori sun tsufa
  • Buhari yana sa rai ‘yan damfara ba za su iya buga jabun sababbin N200, N500 da N1000 da aka yi ba

Abuja - Muhammadu Buhari yayi karin bayani a game da abin da ya sa aka canza manyan takardun kudi, aka fito da wasu sababbin Nairori a Najeriya.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba 2022, inda aka ji shugaban kasar yana cewa kudin da ake amfani da su, sun dade.

Shugaba Muhammadu Buhari yace kusan tsawon shekaru 20 kenan ana amfani da N200, N500 da N1000.

A dalilin tsawon lokacin da gwamnatin Najeriya ta dauka ba tare da sake buga kudi ba, takardun Nairorin da ake da su sun fita daga cikin hayyacinsu.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane, Sun Ce da Sababbin Kudi Za a Biya Fansar N5m

Masu kudin jabu

Da yake kaddamar da sababbin kudin a wajen taron majalisar zartarwa na FEC a fadar Aso Villa, Buhari yace za ayi maganin masu buga kudin jabu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda Mai girma shugaban Najeriyan yake fada, sababbin kudin da aka fito da su za su yi wa masu sana’ar buga kudin bogi wahalar satar irinsu.

Sababbin kudi
Sababbin kudin da aka buga Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

An yi wa sababbin takardun kudin amfani da tsari na tsaro da zai sa ya yi wahala a iya buga jabunsu. Hakan zai sa kudin karya su daina yawo a kasuwa.

A Najeriya aka yi aikin

A jawabin da Muhammadu Buhari ya fitar ta bakin Hadiminsa watau Femi Adesina, shugaban kasar ya yi farin ciki da kamfanin gida ya yi wannan aiki.

A jawabin na Femi Adesina, Buhari yayi bayanin abin da ya sa ya amincewa gwamnan babban banki na CBN ya buga sababbin₦‎200, ₦‎500 da ₦‎1000.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Bayyana Muhimman Dalilan da Suka da Ya Sake Fasalin Takardun Naira

Jawabin shugaban kasar ya nuna tsarin Duniya shi ne duk bayan shekaru biyar zuwa takwas, hukuma ta fito da sababbin kudi ko a canza masu fasali.

This Day tace sauran dalilan da suka jawo aka canza kudin sun hada da tsare martabar kasa, sa kudi su rika zagayawa, da rage adadin takardun kudi.

Masu garkuwa da mutane

Rahoto ya zo cewa an sace Bayin Allah a Kauyen Zamfara, mutanen gari suna yin karo-karo domin su tattara kudin da za a ceto su daga hannun miyagu.

A daidai lokacin da ake neman inda miliyoyin za su fito sai ‘yan bindigan suka ce ba za su karbi tsofaffin kudin da ake canzawa ba, sababbin kudi suke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel