Waiwayen Tarihi: Lokuta 11 Da Aka Yiwa Kudin Najeriya Sauye-Sauye Daga 1960

Waiwayen Tarihi: Lokuta 11 Da Aka Yiwa Kudin Najeriya Sauye-Sauye Daga 1960

A ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba, Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa tarihi matsayin shugaban Najeriya na biyu da ya sauya fasalin kudin Najeriya sau biyu; na farko da mulkin Soja, na biyu Demokradiyya.

Shugaban kasan ya bayyana sabbin kudin Naira N200, N500 da N1000 a taron majalisar zartaswa dake gudana kulli Laraba a fadar Aso VIlla dake Abuja.

Gabaninsa, tsohon shugaba Olusegun Obasanjo shima ya fitar sabbin kudi lokacin mulkin soja tsakanin 1976 da 1979 sannan lokacin demokradiyya tsakanin 1999 da 2007.

Wannan ba shine karon farko da aka canza kudin Najeriya ba.

Kudin farko da aka fara amfani a Najeriya shine Shillings a 1880 karkashin turawa mulkin mallaka.

Kudade
Waiwayen Tarihi: Lokuta 11 Da Aka Yiwa Kudin Najeriya Sauye-Sauye Daga 1960 Hoto: Preseidency
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

N165bn sun dawo: CBN ya ce sabon kudi ya fara yawo, sabon batu mai muhimmanci ya fito

Ga jerin lokutan da aka yiwa kudin Najeriya sauya tun bayan samun yanci a 1960:

1. A 1962, an sauya sunan "Tarayyar Najeriya" dake kan kudin zuwa "Tarayyar Jamhuriyyar Najeriya" domin nuna cewa Najeriya ta zama jamhuriyya mai zaman kanta.

2. A 1973, an sauya kudin Najeriya daga ' Sheilling da Fam' zuwa 'Kwabo da Naira'. A lokacin kwabo 100 na daidai da Naira 1.

3. A 1977, an buga sabin kudi N20 da hoton tsohon shugaban kasa Janar Mutala Mohammed.

An buga kudin ne lokacin saboda fadadar tattalin arzikin kasar.

4. A 1979 aka buga takardun N1, N5, da N10 kamar yadda akayi na N20.

5. A 1984, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauya kalolin dukkan kudaden illa 50 Kobo

6. A 1999, shugaba Obasanjo ya fitar da sabon kudin N100; a Nuwamba 2000 akayi N200, a Afrilu 2001 aka buga N500, sannan a Oktoba 2005 aka buga N1000

Kara karanta wannan

Bayan Sauyin Launi, Buhari Ya Nuna Inda Sababbin Kudin da Aka Yi Suka Bambanta

7. A 2007, aka mayar da N20 kudin leda, sannan aka sauya bugun silallan N1, N2 da 50kobo

8. A 2009, aka mayar da kudin N50, N10 da N5 kudin leda kamar yadda aka yiwa N20 a baya

9. A 2010, Domin murnar cikar Najeriya shekaru 50 da samun yancin kai, Goodluck Jonathan ya buga sabon kudin N50.

10. A ranar 19 ga Disamba 2014, Gwamnatin Jonathan ta buga sabbin kudin N100 domin murnar cikar haduwar Arewa da Kudu shekaru 100 a tarihin Najeriya.

11. A ranar Laraba, 23 2022 ga watan Nuwamba,2022 Shugaba Muhammadu Buhari sauyin fasalin kudin Naira N200, N500 da N1000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel