Sababbin kudi: EFCC da ICPC Za Su Sa Ido Kan Masu Cire Makudan Kudi Inji CBN

Sababbin kudi: EFCC da ICPC Za Su Sa Ido Kan Masu Cire Makudan Kudi Inji CBN

  • Gwamnan CBN yace yanzu mutum bai isa ya je banki ya nemi cire makudan kudi daga asusunsa ba
  • Godwin Emefiele ya tabbatar da cewa kafin a iya daukar kudi masu yawa, sai an karbi bayanan mutum
  • Wannan zai ba hukumomi irinsu ICPC da EFCC damar sanin duk inda aka shigar da wadannan kudi

Abuja - Gwamnan babban bankin kasa na CBN, Godwin Emefiele yace za su yi aiki da jami’an hukumomin EFCC da ICPC wajen zura idanu a bankuna.

Guardian ta rahoto Godwin Emefiele yana mai cewa za su hada-kai da wadannan hukumomi domin a rika bibiyar wadanda ke cire kudi masu yawa.

Mista Emefiele ya yi wannan bayani a sa’ilin da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja a wajen bikin kaddamar da sababbin kudin da aka buga.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane, Sun Ce da Sababbin Kudi Za a Biya Fansar N5m

Gwamnan babban bankin yake cewa adadin kudin da mutum zai iya cirewa daga asusu a cikin banki zai ragu saboda tsare-tsaren da CBN zai kawo.

Kudi zai rage yawo a gari

Wannan yana cikin kokarin CBN na ganin kudin da ke yawo a hannun jama’a ya ragu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan dole sai mutum ya cire kudi masu yawa daga asusun banki, Emefiele yace za a hada shi da tulin takardu da zai cike saboda a dauki bayanansa.

Sababbin kudi
An fito da sababbin kudi Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Da zarar mutum ya shiga banki ya karbi masu yawan gaske, za a shiga bin sahunsa domin tabbatar da cewa ba wani aikin assha zai yi da wadannan dukiyar ba.

“Za mu rage adadin kudin da mutane za su iya cirewa a cikin banki. Idan kana neman kudi da yawa, sai ka cika fam barkatai – bila-adadin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Inda aka Samu Cikas, Maganar Taron Dangi da Peter Obi Ta Wargaje

Za mu dauki bayananka, daga BVN zuwa NIN ta yadda jami’an hukumomin EFCC da ICPC za su iya bibiyarka, a ga aikin da za ayi da kudin.

- Godwin Emefiele

Ba wani ake hari ba - CBN

Punch ta rahoto Gwamnan babban bankin yana cewa ba a shigo da wannan tsari saboda ayi kokarin ganin bayan kowa ba, illa iyaka a samar da gyara.

A lokutan baya, Emefiele yace an nemi a buga sababbin kudi, amma wasu suka hana hakan tabbata. Sai a shekarar nan ne dai maganar ta zama gaskiya.

Babu maganar buga jabu

Rahoto ya zo cewa Muhammadu Buhari yace a Najeriya aka buga sababbin kudin, ya kuma yi bayanin fa’idojin da za a samu a dalilin canjin da aka yi.

Dama can a kowane shekaru 5 zuwa 8 ake bukatar a fito da sabon kudi, Muhammadu Buhari yace takardun da aka sauya sun fi shekaru 20 a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Asali: Legit.ng

Online view pixel