Kwankwaso: Inda aka Samu Cikas, Maganar Taron Dangi da Peter Obi Ta Wargaje

Kwankwaso: Inda aka Samu Cikas, Maganar Taron Dangi da Peter Obi Ta Wargaje

  • Rabiu Musa Kwankwaso mai ya yi karin haske a game da sabaninsu da LP a lokacin da aka nemi a hade
  • ‘Dan takaran na New Nigeria Peoples Party (NNPP) yace an dage cewa Peter Obi ne za a ba tikitin 2023
  • Kwankwaso yace bangaren LP ba su yarda ayi la’akari da shekaru da rike mukamai wajen bada takara ba

Lagos - Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin NNPP ya sake magana a kan dunkulewarsu da ‘yan jam’iyyar LP.

Jaridar The Guardian ta rahoto Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana cewa ba za ta yiwu jam’iyyar NNPP tayi tafiya da LP ba saboda sabani da aka samu.

‘Dan takaran shugaban kasar ya yarda cewa da sun yi taron dangi, zai fi sauki suyi nasara, yace wasu sun nuna dole a ba 'Dan kudu maso gabas takara.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka bijiro masa da maganar yayin da ya tattauna da kungiyar ‘yan jarida na kasa kwanaki a garin Legas.

Lokaci ya kure a yanzu - Kwankwaso

Tsohon Gwamnan na jihar Kano yake cewa ya yi mamaki da ya ji wasu suna dauko wannan magana a halin yanzu bayan damar yin hakan ta shude masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Kwankwaso yace da hakan ta tabbata, INEC ba za ta rika tunanin kai zabe zuwa zagaye na biyu ba, tun a tashin farko za a san wanda ya yi nasara.

Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da Isaac Idahosa a Ribas Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

“Mun wuce lokacin da za a hada wata alaka. Amma hakan abu ne mai kyau. Da an yi nasara, INEC ba za ta rika maganar kai zabe zagaye na biyu ba.
Inda aka samu tababa shi ne a game da wanda za a ba takarar shugaban kasa da wanda za a tsaida ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Hakura da Maganar Cin Zaben 2023 – Kwankwaso Ya Jero Dalilan faduwar PDP

Kwamitin duka jam’iyyun sun zauna suka yi la’akari da shekaru, ilmin boko, da mukaman da aka rike, amma kwamitin LP ba su yarda da wannan ba."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Abin ba son kai ba ne

A cewar Kwankwaso, an sa son kai a lamarin, ana ganin ba a taba samun shugaban kasa daga Kudu maso gabas ba, don haka dole ne sai an tsaida Peter Obi.

Kwankwaso wanda yake harin mulki a zaben shekara mai zuwa yace a tsarin mulki, mutum ba zai iya zama shugaban kasa ba, sai ya samu 25% a jihohi 25.

Kwankwaso a Ribas

Da ya je Ribas domin bude ayyukan Gwamnatin Jihar, an samu rahoto Rabiu Musa Kwankwaso ya yabi Nyesom Wike a kan rikicinsu da Atiku Abubakar.

Rabiu Kwankwaso yace babu yadda PDP za ta karbe shugabancin Najeriya alhali ba ta da goyon baya sosai a manyan jihohi irinsu Legas, Kano da Ribas.

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

Asali: Legit.ng

Online view pixel