Shugabancin kasa na 2023: Afenifere Ta Aika Muhimmin Sako Ga Yankin Arewa

Shugabancin kasa na 2023: Afenifere Ta Aika Muhimmin Sako Ga Yankin Arewa

  • Kungiyar kabilar yarbawa ta Afenifere, ta ba yarda cewa adadin mutanen da ke arewa sun yi na sauran yankuna ba
  • Cif Ayo Adebanjo, shugaban kungiyar, ya bayyana kallon da ak yi wa arewa tafi sauran yankuna yawa a matsayin zamba kuma bai yarda da hakan ba
  • Ya aika muhimmin sako ga manyan yan siyasan arewa yana mai cewa yankin ba za ta zama mai zaben wanda zai mulki Najeriya ba

Legas, Victoria - Cif Ayo Adebanjo, shugaban Afenifere, kungiyar yarbawa a kudu maso yammacin Najeriya, ya aika sako mai muhimmanci ga yankin arewa gabanin babban zaben 2023.

Kamar yadda Punch ta rahoto, Cif Adebanjo, a sakonsa ga arewa, ya ce ba yankin ne za ta rika zaba wa yan Najeriya shugaban kasa ba yayin zabe.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

Adebanjo
Shugabancin kasa na 2023: Afenifere Ta Aika Muhimmin Sako Ga Yankin Arewa. Hoto: Afenifere.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana hakan a ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba, yayin gabatar da kasida a Cibiyar Harkokin Kasa da Kasa ta Najeriya da ke Victoria, Island, Legas, rahoton The Cable.

Cif Adebanjo ya ce:

"An ce dole kudu maso gabas ta zo ta tattauna da arewa saboda siyasa batu ne na yawan mutane. Abin da na ke cewa shine - kuma na fada wa mutane jiya - ba alfarma kudu ya kamata su nema ba; hakkinsu ne. "Amma duk lokaci sai in ji ana cewa su tafi wurin arewa saboda su ke da yawan mutane, yawan mutane na zamba? Ba za ka iya sayar min da hakan ba.
"Sun fada mana mu yi aiki tare amma saboda yanzu su ke da shugaban kasa mai ci, sun ce 'ba wanda zai iya zama shugaban kasa sai ya zo arewa kuma abin takaici wasu yan kudu sun yarda an rude su cewa ba za su iya komai ba sun durkusawa arewa, ban yarda da hakan ba."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya tona sirrin gwamnoni, ya ce ba zai yi Allah wadai da wata kasurgumar kungiyar ta'addanci ba

Shugaban na Afenifere ya kara da cewa Arewa ba ta da hurumin zama wacce za ta rika zaben wanda zai zama shugaban kasa, yana mai cewa dukkan yankuna komin kankantarsu ne ya kamata su zabi shugaban kasar tare.

Ya ce an gina Afenifere ne kan adalci da tafiya tare da kowa ba tare da son rai ba.

Dattawan Arewa sun yi magana kan hadin kan Najeriya

Kazalika, kungiyar dattawan arewa ta ce wadanda ke cewa batun hadin kan Najeriya ba abin sassanci bane ba su tare da arewa.

Dr Hakeem Ahmed, direktan watsa labarai na NEF na kasa, ya ce:

"Hadin kan Najeriya abu ne da za a iya tattaunawa kansa. Sai dai ka sassanci saboda kasashe na da rauni kuma dole ka kula da su da bukatunsu ko kuma su karye kuma muna daf da karyewa wa."

Tinubu Ya Isa Akure Don Ganawa Da Shugabannin Afenifere

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya isa Akure, babban birnin jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Shin Najeriya kasar addini ce? Jigon siyasan Arewa ya bayyana matsayin Najeriya game da addini

Tinubu wanda ya isa jihar a yau Lahadi, 30 ga watan Oktoba, zai gabatar da manufofinsa ga Pa Reuben Fasoranti da shugabannin kungiyar Yarbawa ta Afenifere, jaridar The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel