'Yan Arewa Basu Isa Suyi Mana Mulkin Mallaka Ba inji Wani Jigon Kudu

'Yan Arewa Basu Isa Suyi Mana Mulkin Mallaka Ba inji Wani Jigon Kudu

  • Kungiyoyin Kabilu dai dama a Nigeria na Ganin Yan Arewa basu yi musu adalci ba wajen fitar da mafi yawan yan takarar shugaban kasa daga yankin su ba
  • Ana ganin cewa har yanzu bata sake zani ba, wajen hadin kan tsakanin yan kasar musamman yan kudanci da arewancinta wajen zaman lafiya
  • A Tsarin Jam'iyyu dai a Nigeria sun dau tsarin fitar da yan takarkaru daga yankin arewa da kudu ko kuma musulmi da kirista

LAGOS: Shugaban kungiyar al’adun Yarabawa ta Afenifere, Cif Ayo Adebanjo, ya ce Arewa ba za ta iya tasarawa sauran ‘yan kasar waye zai zama shugaban kasa ba. .

Adebanjo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin gudanar wata lacca mai taken, ‘Kishin kasa da gina kasa a tarihin Najeriya,’ da aka gudanar a Cibiyar Harkokin Kasa da Kasa ta Najeriya da ke Victoria Island, Legas.

Ayeye
'Yan Arewa Basu Isa Suyi Mana Mulkin mallaka Ba inji Wani Jigon Kudu Hoto: Guardian
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce,

“dole ne kowanne dan kasa daga yankin kudu maso gabas ko yankin arewa koma wanne yanki ne, ace yana da damar da zai iya fitowa a zabe shi ko ya zaba. Kuma dole ne ace kowa yana da dama yadda za'iya yin takarar ko fitowa da dan takara"

Jaridar The Punch Tace Shugaban Ya kara da cewa

“Suna cewa muyi aiki tare amma abin takaici saboda a yanzu sun samar da shugaban kasa a kan mulki, sai suka ce ‘ba wanda zai iya zama shugaban kasa sai ka nemi goyan bayan dan Arewa, kuma abin takaici wasu ‘yan kudu sun yarda da haka cewa dole sai sun bi dan arewa kafin samun mulkin"
“wanne abu arewa ke takama da shi da zata gindaya sharadin, gashi sun tilasta muku kuma kun amince. Don haka in de ana so ci gaba da zama da dorar da zaman lafiya, to dole a gimarma kowanne yanki da nasa ka'idojin".

Shugaban kungiyar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor, a jawabinsa na bude taron, ya bayyana cewa, tun bayan samun ‘yancin kai, babu wani zamani na shugabannin Najeriya da suka iya samar da yanayi na sahihanci don tabbatar da kasancewar Najeriya na samun makomar siyasa a matsayin kasa daya.

Ya ce,

“Kwanan nan, wasu shugabannin siyasar Najeriya sun ce hadin kan Najeriya ba zai yiwu ba,. Wannan wani abin ban mamaki ne domin da alama wadannan shugabannin sun manta da tarihin Najeriya ko kuma sun kasa koyon darasin tarihi nata.
“Haɗin kan Najeriya ba shakka abin tattaunawa ne kuma dole ne a sake tattaunawa domin kawo mafita ko tsira daga kuncin da ake ciki. Haƙiƙanin gaskiya cikin shekaru da yawa akwai abin cewa duk da ƙoƙarin da shugabanninmu na baya ko na yanzu suka yi, haɗin kan Nijeriya bai tabbata ba yadda ake tunani ba.

A nasa bangaren, Daraktan Yada Labarai na kungiyar Dattawan Arewa, Dr Hakeem Ahmed, ya ce,

“Wasu shugabannin siyasar Najeriya sun ce hadin kan Najeriya ba zai yiwu ba. Ban san su wane ne wadannan ba, amma zan iya gaya muku ba ’yan Arewa ba ne kuma ba su da alaka da arewa.
“Haɗin kan Najeriya abu ne na tattaunawa. Ko dai ku sasanta saboda al'ummomi suna da rauni sosai kuma suna da hankali sosai kuma dole ne ku kula da su kuma ku kula da bukatunsu ko kuma sun karya kuma mun kasance a wannan lokacin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel