Najeriya Ba Kan Ka’idojin Addini Ake Mulkinta Ba, Inji Jigon APC Marafa

Najeriya Ba Kan Ka’idojin Addini Ake Mulkinta Ba, Inji Jigon APC Marafa

  • Sanata Marafa na jihar Zamfara ya bayyana matsayar APC game da addini da siyasa a Najeriya
  • Ya bayyana cewa, Najeriya ba kasa ce ta addini ba, don haka babu wata matsala game gamin Tinubu da Shettima
  • Kiristocin Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da yadda APC ta zabo Muslmai biyu a kujerun shugaba da mataimaki a zaben 2023

Jihar Zamfara - Kodinetan kamfen na jam'iyyar APC, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana cewa, babu wata illa ga turbar APC na hada Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista a kujerun takara.

Ya kuma bayyana cewa, duk mai kokarin sukar jam'iyyar kan wannan lamari tabbas ba komai a gabansa illa munafunci.

Marafa, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau ya shaidawa jama'a cewa, jam'iyyar ta shirya cin zaben 2023 mai zuwa, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

A cewarsa, APC a kullum burinta shine hada kan jama'a musamman mambobinta. Ya kuma shaida cewa, bai kamata a yaudari 'yan Najeriya ba, domin ba kasa ce da ake mulka a turbar addini ba.

Jigon siyasan Arewa ya fadi matsayar Najeriya game da addini
Najeriya Ba Kan Ka’idojin Addini Ake Mulkinta Ba, Inji Jigon APC Marafa | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Najeriya ba kasar addini ba bace

A cewarsa:

"Babu wanda zai yaudare mu, ba a mulkin Najeriya a tafarki na addini. Akwai jam'iyyun siyasa 18 a Najeriya.
"Idan wata jam'iyya tace za ta yi tikitin Kirista da Kirista wata kuma tace za ta yi na Musulmi da Musulmi, ka bar wacce ta yi abin da baka so ka bi wacce ta yi abin da kake so. Meye abin damuwa?"

Marafa ya kuma tabbatar wa 'yan Najeriya cewa, jama'ar Zamfara za su kawo sama da 25% na kuri'un da dan takarar shugaban kasa na APC ke bukata a zaben 2023, Daily Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Na Fasa: Ana Gab Da Daurin Aure, Ango Yace Ya Fasa Bayan Gano Amaryar Na Da 'Yaya 2

Tsohon sanatan mai wakiltar Zamfara ta tsakiya ya ce, yankin Arewa maso Yamma yanki ne mai karfi ga APC, kuma tabbas za ta yi nasara a zaben badi.

Dan Tinubu ya jagoranci matasa don tallata APC a Kano

A wani labarin kuma, dan Tinubu ne ya jagoranci matasa a jihar Kano domin gudanar da gangamin tattara masoya a jihar.

An ga hotunan lokacin da Seyi ke tare da matasa suna gangami a kwaryar Kano.

Ba wannan karon ne farko da aka samu da ga dan siyasar Najeriya ya fito don taya mahaifinsa gangamin kamfen ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel