Mazauna Zamfara sun ce an san inda su Bello Turji suke bayan saka tukwicin N95m ga wanda ya fallasa shi

Mazauna Zamfara sun ce an san inda su Bello Turji suke bayan saka tukwicin N95m ga wanda ya fallasa shi

  • Jama'ar yankunan da 'yan bindiga suka addaba sun fito sun bayyana ra'ayinsu ga yunkurin sojoji na ayyana neman su Turji ruwa a jallo
  • Sojoji sun sanya tukwici mai gwabi ga duk wanda ya ba da masaniyar da ta kai ga kame 'yan ta'adda 19 a Najeriya
  • Jihohin Arewacin Najeriya ne suka fi shiga tashin hankalin rikicin 'yan bindiga a Najeriya a shekarun nan

Zamfara - Wasu mazauna a jihar Zamfara a ranar Litinin sun bayyana shakku kan samun wani ci gaba a yunkurin sojoji na ayyana neman 'yan ta'adda ruwa a jallo, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kuma bayyana mamakin cewa, meye ya dauki sojojin Najeriya dogon lokaci kafin ayyana neman shugabannin 'yan ta'addan ruwa a jallo ko kuma ma kokarin kama su da ransu.

Idan baku manta ba, wani rahotonmu na baya ya bayyana yadda aka ambaci wasu tsagerun 'yan ta'adda 19 da sojoji suka ce suna nema ruwa a jallo tare da sanya tukwici mai gwabi ga wanda ya fallasa maboyarsu.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Saki Sunaye Da Hotunan Shugabannin 'Yan Ta'adda 19 Da Ake Nema Ruwa A Jallo, Tare Da Tukwicin N5m

Wadannan 'yan ta'adda dai sun dade suna cin karensu babu babbaka a yankunan Arewa masu Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

An san maboyar su Bello Turji, inji 'yan Zamfara
Mazauna yankuna sun ce an san inda su Bello Turji suke bayan saka ladan N95m ga wanda ya fallasa shi | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rundunar ta ce, duk wanda ke da masaniya na yadda za a kama tsagerun nan za a bashi N5m, ga kuma lambar waya kamar haka 09135904467 don kiran sojoji.

Martanin mazauna yankunan da abin da ya shafa

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, wani mazaunin Zamfara, Mustapha Shinkafi ya ce, maimakon ayyana neman 'yan ta'adda ruwa a jallo, kamata ya yi sojojin su hallaka su kawai.

Ya ce:

"Dan bindiga mai makami kamar Bello Turji da sauran 'yan ta'adda na ta zirga-zirga daga wannan kauyen zuwa wani, musamman a kananan hukumomin Shinkafi da Maradun na jihar Zamfara da kuma kananan hukumomin Isa da Sabon Birni a jihar makwabta Sokoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Fitattun Malamai Biyu a Jihar Arewa

"Turji ya gina katafaren gida mitoci kadan daga yankin Fakai kuma a cikin gidan yake rayuwa har sai da sojojin saman Najeriya suka farmake shi suka lalata gidan.
"Ayyana neman 'yan ta'adda ruwa a jallo ba zai sauya komai ba. Abu daya da zai inganta tsaro ya kare rayuka da dukiyoyi shine hallaka 'yan ta'addan."

'Yan sanda sun ayyana neman kasurgumi Ado Aliero ruwa a jallo a baya

Wani mazaunin yankin, Musa Hassan ya bayyana cewa, 'yan sanda sun ayyana neman shugaban 'yan ta'adda Ado Aliero ruwa a jallo tare da alkawarin tukwici ga wanda yasan maboyarsa jim kadan bayan da ya farmaki kauyen Kadisu a Faskari ta jihar Katsina.

Ya kara da cewa:

"Tun wancan lokacin, Ado Aliero na yawo ba tare da wata matsala ba kuma yana yankin Yandoto inda aka ba shi sarauta watannin baya. A ra'ayina, kamo su, ba wai ayyana nemansu ba shine abin da ya fi dacewa."

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Arewa yayin da 'yan bindiga suka sace wani Limamin Katolika

Wani kuma, Aliyu Zurmi cewa ya yi:

"Dankarami ya sanya mazauna kananan hukumomin Zurmi da Birnin Maga a jihar Zamfara da wasu yankunan Katsina cikin tashin hankali. Amma a haka yake cin fariyar babu wanda ya isa ya yi masa wata barazana."

Rahotonmu na baya ya bayyaa jerin 'yan ta'addan 19 da rundunar sojin Najeriya ta ce su take nema ruwa a jallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel