Sojoji Najeriya Sun Kashe ’Yan Ta’adda da Dama a Jihar Kaduna

Sojoji Najeriya Sun Kashe ’Yan Ta’adda da Dama a Jihar Kaduna

  • Rundunar sojin Najeriya ta bayyana wasu ayyuka da ta yi a yankunan jihar Kaduna, Arewa maso Yammacin Najeriya
  • An hallaka 'yan bindiga da dama tare da fatattakarsu a yankuna daban-daban na jihar a 'yan kwanakin nan
  • An kwato makamai da wasu kayayyaki daban-daban na aikata laifuka a hannun 'yan ta'addan da suka tsere

Jihar Kaduna - Rundunar sojin Najeriya na sashe na 1 da a jihar Kaduna sun share yankunan Maidaro, Kagi Hill, Kusharki da Anguwan Madaki a karamar hukumar Birnin Gwari daga 'yan ta'adda.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, birgediya janar Onyema Nwachukwu ya fitar, inda yace an kashe 'yan bindiga hudu kana wasu da dama sun tsere.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Kama Kwamandan Yan Bindiga, Sun Kashe Mayaka 8 A Wata Jihar Arewa

Yadda sojoji suka ragargaji 'yan ta'adda a Kaduna
Sojoji Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda da dama a jihar Kaduna | Hoto: ait.live
Asali: UGC

Kayayyakin da aka kwato daga hannun 'yan bindiga

A bangare guda, an kwato bindigogi kirar AK-47 guda bakwai da kuma wasu bindigogi masu sarrafa kansu guda uku, AIT ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, an kwato wasu kananan bindigogi 6, da wasubindigogu hadin gida guda uku da babura hudu da dai sauran kayan aikata laifuka.

A wasu ayyukan da sojojin suka yi a Sabon Birnin-Zartake, Ungwan Lima Riyawa da Tungan Madaki na jihar, a nan ma sun hallaka 'yan bindiga da dama tare da fatattakar wasu adadi.

A cewar sanarwar, dakarun sojoji sun tarfa wasu 'yan bindigan dake kokarin tserewa a Kagi Hill, an hallaka tsageru uku bayan barin wuta, rahoton Tribune Online.

Rundunar sojin ta bayyana cewa, wadannan ayyuka sun yiwu ne sakamakon aikin hadin kai da aka samu tsakanin sojojin sama da na kasa da sauran jami'an tsaro a jihar ta Kaduna.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

Jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da kokarin kakkabe yankunan kasar nan daga mamayar 'yan ta'adda dake sace-sace da kisan gilla kan mazauna.

Mata Na Ba ’Yan Bindiga ’Ya’yansu Mata Saboda Kudi, Inji Kwamishinar Kaduna

A wani labarin, Hafsat Baba, kwamishinar ayyukan jama'a ta jihar Kaduna ta bayyana cewa, yana da matukar muhimmanci a magance wasu matsaloli da suka dumfaro mata a jihar.

Ta bayyana cewa, akwai matan dake tura 'ya'yansu mata ga 'yan ta'adda saboda kawai su samu kudin kashewa, rahoton TheCable.

Hafsat ta bayyana hakan ne a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba a tattaunawa ta 22 na majalisar kasa kan harkokin mata da ya gudana a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel