Bankin Duniya Ya yi Hasashe Mai Ban Tsoro Game da Halin da Najeriya Za ta Shiga

Bankin Duniya Ya yi Hasashe Mai Ban Tsoro Game da Halin da Najeriya Za ta Shiga

  • Masanan da ke Bankin Duniya su na ganin za ayi fama da matsalar kayan abinci a shekara mai zuwa
  • Ambaliyar ruwa da rashin kyawun kayan amfanin gona za su jawo abinci ya yi tsada a Najeriya
  • Baya ga matsalar abinci, za ayi fama da karyewar darajar Naira da kuma wahalar fetur da Kirismeti

Abuja - Bankin Duniya ya yi hasashen cewa faduwar darajar kudin Najeriya da sauran kasashe yana da mummunan tasiri ga tattalin arzikinsu.

Punch ta kawo rahoto cewa binciken babban bankin Duniya yace karyewar Naira zai jawo a samu matsalar tsadar man fetur da tashin kayan abinci.

Binciken ya tabbatar da cewa yanzu haka Najeriya da irin wadannan kasashe su na cikin matsi a sakamakon ambaliyan ruwa da hauhawar farashi.

A gefe guda, masu ciniki da Dalar Amurka sun samu sauki a ‘yan kwanakin nan bayan tashin gwauron-zabin da kaya suka yi ya fara zuwa karshe.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da Gwamna El-Rufai ya yafewa wasu fursunoni hudu saboda wani dalili

Bankin Duniyan yace yakin da ake yi tsakanin Sojoji Rasha da na kasar Ukraine tun farkon shekarar nan ya jawo mai ya tashi a kasuwannin Duniya.

Bankin da ke birnin Washington a kasar Amurka yace 90% na kasashen Duniya sun gamu da tashin farashin alkalama da wasu daga cikin kayan abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gona.
Gona a jihar Kwara Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tashin da fetur da dizil ya yi, ya haddasa tsadar kayan amfanin gona a farkon kakar shekarar nan. Mun fahimci a wasu wurare ana satar kaya a gonaki.

Rahoton yace binciken ya nuna an samu hauhawar farashin abinci da kimanin 12% zuwa 15% a Kasashen Afrika, tsakiyar Asiya da Gabashin kasar Turai.

A kasashen Kudancin Asiya, farashin kaya zai tashi da fiye da 20%. Lamarin zai fi sauki a kasashen Amurka, Arewacin Afrika da kuma gabas ta tsakiya.

Za a cigaba da wahalar man fetur

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari Ya Jagoranci Taron Tsaro Na Gagggawa

A wani rahoton dabam, jaridar tace babu mamaki jama’a suyi bukukuwan kirismeti da na sabuwar shekara ta 2023 a cikin wahalar fetur a jihohin Najeriya.

Masu jirage su na barazanar daina aiki saboda bashin $90m da suke bin kamfanin NNPC. Kudin da ‘yan kasuwa ke bin gwamnati ya taru sosai a wata tara.

Clement Isong, wanda shi ne Sakataren kungiyar ‘yan kasuwan mai, yace ana sa rai NNPC za ta magance wannan matsala da masu jigilar mai suke kokawa.

$1 ta kai N818

A kasuwannin canji, kun ji labari a farkon makon nan cewa Naira tana kara fita daga hayyacinta ne yayin da Dalar Amurka da sauran kudin ketare suke tashi.

Ana tunanin sanarwar da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bada na canza manyan takardun kudi, ya jawo Naira ta sa Dala tana kara wahala sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel