Gwamna El-Rufai Ya Yafewa Fursunoni Hudu Saboda Tuna Ranar ’Yancin Kai

Gwamna El-Rufai Ya Yafewa Fursunoni Hudu Saboda Tuna Ranar ’Yancin Kai

  • Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana yafewa wasu fursunoni hudu dake zaman gidan kaso a jihar Kaduna
  • Gwamnan ya yafe musu ne albarkacin zagayowar ranar 'yancin kai ta Najeriya, ya fadi kuma wani dalilin
  • A wannan shekarar ne Najeriya ta cika shekaru 62 da samun 'yancin kai, jama'a da dama na murna

Jihar Kaduna - Gwamna Mallam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yafewa wasu fursunoni hudu a bikin tunawa da ranar 'yancin kan Najeriya karo na 62 bisa ikon da kundin tsarin mulkin kasa ya bashi.

A cikin wata sanarwa da aka fitar daga gidan gwamna na Sir Kashim Ibrahim, an bayyana sunayen mutanen hudu da gwamna ya yafewa, rahoton TheCable.

El-Rufai ya yafewa wasu fursunoni 4
Gwamna El-Rufai ya yafewa fursunoni biyu saboda tuna ranar 'yancin kai | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sun hada da Abdullahi Haruna, Usman Ahmed, Mohammed Sani da Khalillullahi Mohammed, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Dan Allah Ku Yafe Mun Kura-Kuran Da Na Yi A Mulkina, Gwamnan Arewa Ya Roki Mutanen Jiharsa

Sanarwar ta bayyana cewa, an yafewa fursnonin hudu ne saboda tausayinsu da gwamna ya ji, kuma hakan ya dace da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, an ce gwamnan ya yi amfani da shawarin kwamitin yafiya na jihar kafin yanke wannan hukunci.

Sanarwar ta ce:

"Wadanda aka yafewan suna kan zaman gidan kaso ne na tsawon shekaru uku da 'yan kai, kuma suna da sauran watanni shida ne ko kasa a gidan yari.
"Gwamna El-Rufai ya bukaci fursunonin da aka yafewa da su kasance masu dabi'a mai kyau yayin da suka koma ga danginsu kuma ga sauran al'umma."

CBN da NMfB Sun Fara Bibiyar Asusun Wadanda Suka Ci Bashin Banki Na Lokacin Korona, Suna Cire Kudi

A wani labarin, babban bankin Najeriya (CBN) da kuma bankin NIRSAL sun fara karbo kudaden da suka ba 'yan Najeriya rance a 'yan shekarun baya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ina Goyon Bayan Sauya Fasalin Naira Dari Bisa Dari, Shugaba Buhari

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, an fara karbo kudaden ne a ranar Juma'a 28 ga watan Oktoban 2022 ta hanyar amfani da lambar bankin bai daya na BVN.

Hakazalika, bankin na NIRSAL zai fara dawo da kudaden da 'yan Najeriya suka karba a lokacin Korona karkashin shirin TCF da kuma na 'yan kasuwa karkashin shirin AGSMEIS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel