Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Gaggawa da Hafsoshin Tsaron Kasa a Abuja

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Gaggawa da Hafsoshin Tsaron Kasa a Abuja

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar gaggawa da hafsoshin tsaro a babbar birnin tarayya Abuja
  • Taron na gudana ne a safiyar yau Litinin, 31 ga watan Oktoba, yayin da ake tsaka da fargaba kan yuwuwar kai hare-hare a birnin kasar
  • Ofishin jakadancin Amurka ta yi gargadi kan yuwuwar kai hare-hare a wasu yankunan babban birnin tarayyar kasar

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taron gaggawa da manyan hafsoshin tsaro na kasa a kan lamarin tsaro.

Kamar yadda mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwar zamani, Buhari Sallau ya sanar a shafinsa na Facebook, taron na gudana ne a safiyar yau Litinin, 31 ga watan Oktoba, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Buhari na jagorantar taron gaggawa
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Gaggawa da Hafsoshin Tsaron Kasa a Abuja Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ana sanya ran za su sake bita da kuma karfafa lamarin tsaro a kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Abinda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Tambayi Kowane Mai Burin Gaje Buhari, Dattawan Arewa

Idan za ku tuna, ofishin jakadancin Amurka ta yi gargadi kan yiwuwar kai hare-hare a wasu yankunan babban birnin tarayya Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan ya haifar da tsoro da fargaba sosai a tsakanin al’umma domin kasashen US da UK sun shawarci yan kasarsu da su bar Abuja.

Sai dai kuma, da take martani kan lamarin, hukumar DSS ta bukaci yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu amma dai su zamo masu lura.

A wata sanarwa daga kakakinta, Dr. Peter Afunanya, DSS ta shawarci yan Najeriya da su yi taka-tsantsan, sai dai ta bayar da tabbacin cewa za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya.

Ta bukaci yan Najeriya da su sanar da hukumar bayanai da ke da nasaba da barazana ko ayyukan da basu yarda da shi ba.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Tsoron Hari, Buhari Zai Yi Ganawar Gaggawa da Shugabannin Tsaro

Sojoji Sun Kama Kwamandan Yan Bindiga, Sun Kashe Mayaka 8 A Wata Jihar Arewa

A wani labari na daban, mun ji cewa dakarun rundunar sojojin sama da na kasa sun kashe wasu yan bindiga guda takwas yayin da suke yunkurin kai mummunan hari kan al'umma a jihar Neja.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa sojojin sun farmaki yan bindigar ne a lokacin da suke kokarin kaddamar da hari a New Bussa, karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Majiyoyi daga garin sun bayyana cewa dakarun sojin hadin gwiwar sun kuma kama kwamandan yan bindigar wanda ya jagoranci kai harin a daren ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel