Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Sakataren Gwamnatin Enugu da Wasu Mutane

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Sakataren Gwamnatin Enugu da Wasu Mutane

  • 'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Sakataren gwamnatin jihar Enugu, Dakta Dan Shere, da wasu matafiya da dama ranar Alhamis
  • Wata majiya tace tsohon SSG na kan hanyar zuwa Nsukka lokacin da maharan suka tare su tare da wasu matafiya
  • A ranar Lahadi da ta gabata ne masu garkuwa suka sace ɗaliban jami'ar UNN kuma har yanzun ba su kuɓuta ba

Enugu - Wasu miyagun 'yan bindiga sun sace tsohon sakataren gwamnatin jihar Enugu, Dakta Dan Shere, da adadi mai yawa na mutane da har yanzun ba'a tantance yawansu ba.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa tsohon SSG ɗin na cikin matafiya da dama da maharan suka yi awon gaba da su a kan Titin Enugu-Ugwuogo Nike-Nsukka, jihar Enugu ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Ɗaliban Fitacciyar Jami'a A Najeriya

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Sakataren Gwamnatin Enugu da Wasu Mutane Hoto: leadership.ng
Asali: Twitter

Dakta Dan Shere, ya yi aikin SSG ƙarƙashin mulkin tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani.

Bayanai sun tabbatar da cewa Dakta Shere, kwararren likita na kan hanyarsa ta zuwa Nsukka domin halartar wani taro lokacin da 'yan bindiga suka farmake shi da wasu matafiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya tace 'yan bindiga da suka kai mutum 8 sun buɗe wuta lokuta da dama gabanin su tattara mutanen zuwa mafakarsu da ba'a sani ba.

"Sun harbi Motarmu sosai, ɗaya daga cikinmu ya samu raunin harsashi amma Direbanmu ya yi kokarin ci gaba da tuƙi. Mun yi nasarar tsira da kai wanda suka harba Asibiti." inji ɗaya daga mutanen da suka tsira.

Shin yan bindigan sun nemi fansa?

An ce masu garkuwan da ake kyautata zaton Fulani Makiyaya ne sun ƙara yawan kuɗin fansar da suka nema kan mutanen da suka sace tun farko ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Umurci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Nnamdi Kanu N500m Kuma A Mayar Da Shi Kenya

"Da farko sun buƙaci miliyan biyu kan ɗaya daga cikin mutanen amma yanzun sun ƙara yawan kuɗin zuwa miliyan N30m. Suna amfani da waya wurin gano waye mutum," inji wata majiya.

Legit.ng Hausa ta gano cewa ɗaliban jami'an Najeriya da ke Nsukka, waɗanda aka sace ranar Lahadi, har yanzun ba su samu kuɓuta ba.

A wani labarin kuma ‘Yan Ta’adda Sun Kai Farmaki Caji Ofis, Sun Tare Babbar Hanya a jahar Zamfara

Yan bindiga sun kai farmaki caji ofis a jihar Zamfara inda suka yi wa ‘yan sanda mazurai tare da kwace musu wayoyinsu da wasu kayayyakinsu masu daraja.

Sun kara da tare manyan titunan jihar Zamfara da suke sadata da jihar Katsina inda suka dinga tare masu ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel