Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Daliban Jami'ar UNN a Hanyar Ta Komawa Makaranta

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Daliban Jami'ar UNN a Hanyar Ta Komawa Makaranta

  • Wasu mahara sun yi awon gaba da matafiya da dama cikinsu harda ɗaliban jami'ar Najeriya dake Nsukka wato UNN a Enugu
  • Bayanai sun nuna cewa tuni masu garkuwan suka nemi iyalai su tattara musu miliyan N30m a matsayin kuɗin fansa
  • Wata majiya tace abun da mamaki aikata wannan ɗanyen aiki a hanyar duba da yawan shingen jami'an tsaro da ke Titin

Enugu - An shiga yanayin tashin hankali a babban titin Ugwuogo Nike-Nsukka, ƙaramar hukumar Enugu ta gabas, jihar Enugu biyo bayan garkuwa da adadi mai yawa na matafiya ranar Lahadi.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa daga cikin waɗanda maharan suka yi garkuwa da su harda ɗaliban jami'ar Najeriya dake Nsukka (UNN) yayin da suke hanyar koma wa makaranta bayan janye yajin aikin ASUU.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha da Wasu Mutane

Jami'ar UNN.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwada Daliban Jami'ar UNN a Hanyar Ta Komawa Makaranta Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Wasu matafiya da suka taki sa'a, waɗanda Allah ya kubutar sun bayyana cewa yan bindigan sun farmaki Motocin Bas na haya kusan Shida, suka tsorata su da harbin bindiga sannan suka yi cikin jeji da su.

Bayanai sun nuna cewa masu garkuwan sun tuntuɓi iyalan mutanen da ke hannunsu, sun nemi Miliyan N30m a matsayin kuɗin fansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya ta shaida wa wakilin jaridar cewa daga cikin waɗanda aka sace harda wata mata daga kauyen Aku, ƙaramar hukumar Igbo-Etiti tare da ɗanta. An ce ɗan ya kubuta amma har yanzun matar na can hannun maharan.

Ya ƙara da cewa wani kwararren Likita da ya samu ya kuɓuta daga hannunsu ya biya makudan kuɗin da ba'a bayyana ba kafin ya shaƙi iskar 'yanci.

Mutumin ya nuna tsantsar mamakin yadda harin ya auku a kan Titin dake da Shingen jami'an tsaro Shida daga Nike zuwa Opi Junction, ƙaramar hukumar Nsukka, jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wani Tsohon Gwamna Kuma Babban Jigon PDP Ya Tsame Kansa Daga Kamfen Atiku 2023

Wane hali ake ciki game da Sace ɗaliban UNN?

Duk da har yanzun ba'a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ba, wani ɗalibin jami'ar UNN da ya nemi a sakaya bayanansa yace:

"Eh tabbatas dagaske ta faru, yan uwan abokin zaman ɗakin abokina da mahifiyarsu sun shiga hannun mutanen. Shi kansa abokina sun yi garkuwa da shi amma ya kubuta."

Yadda DSS Da Sojojin Amurka Suka Kai Sameme Suka Kama 'Yan Ta'adda' A Wani Gida A Abuja

A wani labarin Jami'an hukumar yan sandan farin kaya DSS da sojojin Amurka sun kama wasu da ake zargi da hannu a ta'addanci a Abuja

Adewale Adenaike, shugaban unguwar rukunin gidaje na phase 3, Trademore Estate, a Abuja ya magantu kan yadda abin ya faru.

Wannan kamen na zuwa ne kwanaki kadan bayan kasashen waje da suka hada da Amurka da Birtaniya sunyi gargadi kan yiwuwar barazanar tsaro a wasu jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan

Wani Bawan Allah Umar, Ya Fara Tattaki da Kafa Zuwa Abuja Domin Nuna Goyon Baya Ga Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel