Kotu Ta Umurci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Nnamdi Kanu N500m Kuma A Mayar Da Shi Kenya

Kotu Ta Umurci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Nnamdi Kanu N500m Kuma A Mayar Da Shi Kenya

  • Nnamdi Kanu ya sake kayar da gwamnatin tarayya da Antoni Janar a kotu kan dawo da shi Najeriya
  • Kotu ta umurci gwamnatin Buhari ta biya tarar miliyoyin kudi na alhakin rike shi tsawon watanni
  • Gwamnatin Buhari a shekarar 2021 ta sankamo Nnamdi Kanu daga kasar Kenya inda ya tafi harkoki

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Umuahia, jihar Abia ta umurci gwamnatin tarayya ta mayar da Nnamdi Kanu inda suka dauko shi a kasar Kenya a watan Yunin 2021.

Nnamdi Kanu shine shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra IPOB.

Bugu da kari, kotu ta umurci gwamnati ta biya Kanu kudi N500 million a matsayin garkuwa da shi da gwamnati tayi da kuma take masa hakki na bil adama.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kada A Saki Nnamdi Kanu, Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Sabon Hukunci

Kanuu
Kotu Ta Umurci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Nnamdi Kanu N500m Kuma A Mayar Da Shi Kenya
Asali: Original

Kotu Ta Wanke Nnamdi Kanu Amma Bata Ce Mu Sakeshi ba, AGF Malami

Antoni-Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, a ranar Alhamis ya yi tsokaci kan hukuncin kotun daukaka kara da ta wanke Nnamdi Kanu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nnamdi Kanu shine jagoran kungiyar rajin kafa kasar Biyafara watau IPOB.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Dr. Umar Jibril Gwandu, ya fitar, Mr Malami ya ce kawai kotu ta wanke Kanu ne amma bata ce a sakeshi

Yace:

"Ofishin Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a ta samu labarin kotun daukaka kara game da Nnamdi Kanu."
"Amma fa a sani, kawai an wanke Kanu ne amma ba'a sake shi ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel