Zamfara: ‘Yan Ta’adda Sun Kai Farmaki Caji Ofis, Sun Tare Babbar Hanya

Zamfara: ‘Yan Ta’adda Sun Kai Farmaki Caji Ofis, Sun Tare Babbar Hanya

  • Yan bindiga sun kai farmaki caji ofis a jihar Zamfara inda suka yi wa ‘yan sanda mazurai tare da kwace musu wayoyinsu da wasu kayayyakinsu masu daraja
  • Sun kara da tare manyan titunan jihar Zamfara da suke sadata da jihar Katsina inda suka dinga tare masu ababen hawa
  • ’Yan ta’addan sun harba mutum daya har sau biyu a kafarsa bayan sun tsayar da direban motar da yake ciki amma Ya ki tsayawa

Zamfara - ‘Yan ta’addan dake barna a jihar Zamfara sun ka farmaki ofishin ‘yan sanda a yankin Magami dake Gusau a ranar Talata kuma sun sace wayoyin ‘yan sandan dake aiki a ranar.

Premium Times ta tattaro cewa ‘yan ta’addan sun hallara yankin ne wurin karfe 3:40 na yamma kuma kai tsaye suka tafi ofishin ‘yan sandan.

Kara karanta wannan

Jiragen NAF Sun Yi Lugude Kan Attajirin ‘Dan Ta’adda Sububu da Mukarrabansa, 30 Sun Mutu

Magami yana daya daga cikin yankunan da ‘yan ta’addan suka addaba a jihar Zamfara. Tsabar farmakin ‘yan ta’addan ya tirsasa mazauna yankin gudun hijira zuwa Gusau, babban birnin jihar.

Wani ‘dan jaridan yankin wanda yake rahoto farmakin da ake kaiwa jihar, Abdul Balarabe, yace ta yuwu wannan harin hanya ce ta aikewa da sako ga jami’an tsaron jihar.

“Daga abinda na gane, ‘yan ta’addan basu raunata kowa ba duk da sun samu ‘yan sanda a ofishin amma sun karba wayoyinsu da sauran muhimman abubuwa tare da barazana.”

Gusau yace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace bayan karbar wayoyi, ‘yan ta’addan sun dinga harbi a sama, lamarin da ya ya da hankalin jama’a kafin su koma cikin daji.

Rufe manyan hanyoyi

Hakazalika, a ranar Talata wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki babbar hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Borno: An yi Mummunar Arangama Tsakanin Mayakan ISWAP da Boko Haram, An Halaka 6

Karin lamurran ta’addanci da hare-hare suna yawaita a kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau, hanyar da ta hada jihar Zamfara da Katsina.

Mazauna yankin sun ce ta zama hanya mai matukar hatsari ga masu ababen hawa da masu wucewa sakamakon ayyukan ta’addanci.

Masu amfani da titin sun ce inda yafi hatsari ya hada da Sheme, Yankara a bangaren titin jihar Katsina da Kucheri, Magazu, Wanzamai a bangaren Zamfara.

A farmakin ranar Talata da aka kai wa masu ababen hawa, Balarabe yace an harbi wani har sau biyu a kafa yayin da direban dake tuka motar da yake ciki ya ki tsayawa bayan ‘yan bindiga sun umarcesa.

“Wurin karfe 1:05 na ranar Talata, ‘yan ta’adda sun fito da yawansu inda suka rufe titi. Mutumin da suka harba yana cikin motar da direba ya ki tsayawa.”

- Yace.

Yace yayin da sojoji suka isa wurin tare da buda titin, ‘yan ta’addan sun tsere ta wata hanyar daji kuma suka sake rufe Wanzamai zuwa Yankara na tsawon mintuna talatin.

Kara karanta wannan

Zamfara: An Damke Masu Samarwa ‘Yan Bindiga Layikan Waya da Maganin Karfin Maza

Wata majiyar tsaro wacce ta bukaci a boye sunanta domin bata da hurumin jawabi ga manema labarai, tace ‘yan ta’addan na amfani da shukokin da aka yi a manyan hanyoyin domin boyewa duk lokacin da jami’an tsaro suka biyo su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai amsa kira da sakon kar ta kwana da aka tura masa ba amma ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda na tare hanya a takardar da ya aikewa jaridar Premium Times.

Asali: Legit.ng

Online view pixel