Budurwa Ta Fasa Asusunta, Ta Ce Mota Venza Za Ta Siya da Kudin da Tara

Budurwa Ta Fasa Asusunta, Ta Ce Mota Venza Za Ta Siya da Kudin da Tara

  • Bayan tattala kudade tun shekarar da ta gabata ta 2021, wata 'yar Najeriya ta fasa asusunta, ta ga ruwan kudade
  • Matar mai suna Innocentia Olisa a TikTok ta fasa wata 'yar karamar akwati, ta zauna zaman kirga kudadenta
  • A karshe, Innocentia ta bayyana cewa, ta tara N291k, kuma ta ci alwashin siyan mota Venza da kudin nata, amma dai tace ba za su isa ba

Wata mata 'yar TikTok ta yada bidiyon yadda ta fasa asusun da ta yi shekara guda tana tara kudi a ciki, ta ba da mamaki.

Innocentia Olisa ta bayyana cewa, ta fara jefa kudi a asusun ne tun shekarar da ta gabata, 2021.

A wani gajeren bidiyon da ta yada, ta ce zuciyarta na bugun uku-uku saboda ta sha jin labarin mutanen dake tara kudi a asusu su wayi gari su ga wayam.

Kara karanta wannan

A Raba Ni Da Matata Kafin Hawan Jini Yayi Ajalina, Magidanci ga Alkali

Budurwa ta tara kudi, za ta siya Venza
Budurwa ta fasa asusunta, ta ce Venza za ta siya da kudin da tara | Hoto: TikTok/@centia_collection
Asali: UGC

A cewarta, ta tara kudaden ne domin samun daman siyan mota kirar Toyota Venza a nan gaba kadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, tononta bai kai ga ruwa ba, domin kwata-kwata abin da ta iya tarawa bai wuce N291k, kudin da bai kamo hanyar Venza ba.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Bidiyon da ta yada dai ya shajja'a da dama, kuma mutane da yawa sun nuna sha'awar fara tara kudi a asusu don gaba.

Ga kadan daga abin da wasu ke cewa:

@Dunford Joseph yace:

"A ina zan smau irin wannan asusu?

@user7225670561787 yace:

"Hmmm Allah ya taimakeni shekara mai zuwa nima zan fara nawa ooo."

@Faniyi Omolara351 tace:

"Allah ya miki albarka ina bukatar fara irin wannan ajiya."

@Sani Hassan Tsaffi yace:

"Kin yi kokarin sosai 'yar uwata."

Tsohuwa Ta Aske Gashin Kan Jikanta, Ta Yi Masa Kwal Kobo a Wani Bidiyo

Kara karanta wannan

Kusan Rabin Tsatsona Daga Najeriya ne, Matar ‘Dan Sarki Charles ta Bayyana Babbar Sirrinta

A wani labarin, wata matar da ta bar danta ga kakarsa ta dawo ta ga abin mamaki yayin da ta ga yadda aka yi masa askin kwal-wal.

Haihxx ta yada wani bidiyo mai daukar hankali a TikTok, tare da cewa ta tafi jami'a ne kuma ta bar yaron domin kakarsa ta kula dashi.

A cewartsa, danta na da tarin gashi tun na haihuwa, kuma ta yada bidiyon lokacin da yake da gashinsa cikakke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel