A Raba Ni Da Matata Kafin Hawan Jini Yayi Ajalina, Magidanci ga Alkali

A Raba Ni Da Matata Kafin Hawan Jini Yayi Ajalina, Magidanci ga Alkali

  • Wani magidanci mai shekaru 27 da aure ya roki kotu da ta tsinke igiyar aurensa da matarsa kafin hawan jinin bakin cikinta ya halaka shi
  • Ya sanar da cewa matarsa bata tambayarsa izini kafin ta fice daga gida, yana gane tayi tafiya ne idan ya ga bata nan
  • Ya kara da bayyana cewa, ma’aikaciyar gwamnatin ce amma bai taba sanin albashinta ba kuma bata taimakawa gidansa da ko sisinta, lamarin da ta musanta

Abuja - Wani miji mazaunin gida mai suna Gyang Gyang ya maka matarsa mai suna Jemima a gaban wata kotun gargajiya dake Nyanya kan cewa bata masa biyayya kuma tana fita babu izininsa.

Mai karar ya bayyana wannan zargin ne a bukatar sakin da ya mika a gaban kotun, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ka Taimaka Ka Aureni ta 10, Kyakyawar Budurwa Ta Roki Ooni na Ife

Raba Aure
A Raba Ni Da Matata Kafin Hawan Jini Yayi Ajalina, Magidanci ga Alkali. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
“A matsayina na namijin gidan, matata ya dace ya sanar da ni idan zata yi tafiya amma sai dai ta fice duk lokacin da taso ba tare da ta fada min ba.
“Ina gane cewa tayi tafiya ne idan ban gan ta a gida ba. Bata bin umarni na kuma bata mutunta ni.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Yace.

Ya kara da bayyanawa kotun cewa matarsa bata taimakawa gidansa.

“Mata ta bata taba taimakon gidan nan ba. Ta bar min komai na dawainiyar yara.
“Ina fama da ciwon sukari da hawan jini. Ta ki bayyana min albashinta.
“Bata bayar da gudumawa wurin tabbatar da walwalar iyalan.”

- Yace.

Wanda ke karar ya roki kotun da ta tsinke igiyar aurensu kafin hawan jini ya halaka shi.

Wacce ake kara mai suna Jemima ma’aikaciyar gwamnati cewa kuma ta halarci kotun tare da musanta dukkan zargin da ake mata.

Kara karanta wannan

Kusan Rabin Tsatsona Daga Najeriya ne, Matar ‘Dan Sarki Charles ta Bayyana Babbar Sirrinta

Alkali Doocivir Yawe ya shawarci mata da mijin da su sasanta kansu inda yace:

“Kun kwashe shekaru 27 kuma aure, a wannan lokacin ya dace a ce kuna morar ritayar ku ne tare da yaranku ba neman saki ba. Don Allah ku yi sasanci kafin in yanke hukunci.”

Daga nan ya dage sauraronw shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamban 2022.

A raba ni da matata kafin in halaka ta - Magidanci ya sanar da kotu

A wani labari na daban, wani tsohon direban tasi mai suna Ganiyu Adenekan, ya bukaci wata kotun gargajiya da ke zama a Ake, Abeukuta da ke jihar Ogun a kan ta tsinke igiyar aurensu mai shekaru 22 da matarsa mai suna Morufat. Kamar yadda yayi ikirari, zai iya kashe ta.

Adenekan ya sanar da kotun cewa aurensu ya kai shekaru 10 cikin rashin kwanciyar hankali da banbance-banbance wadanda aka kasa shawo kansu. Ya ce Morufat na son halaka shi don haka a tsinke igiyar aurensu tun kafin yayi nasara a kanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel