Kusan Rabin Tsatsona Daga Najeriya ne, Matar ‘Dan Sarki Charles ta Bayyana Babbar Sirrinta

Kusan Rabin Tsatsona Daga Najeriya ne, Matar ‘Dan Sarki Charles ta Bayyana Babbar Sirrinta

  • Surukar Sarki Charles na Ingila, Meghan Markle, ta bayyana cewa akwai jinin Najeriya a jikinta domin tana da nasaba da kasar
  • Meghan wacce mata ce ga Yarima Harry ta ce gwajin kwayoyin halitta da ta yi shekarun baya ya nuna ita yar Najeriya ce da kaso 43 cikin dari
  • Sai dai ta ce bata san daga kabilar da ta fito ba amma za ta zurfafa bincike don gano salsalarta

Matar ‘dan sarkin Ingila, Meghan Markle, ta bayyana cewa binciken kwayar halitta da tayi ya nuna cewa kaso 43 na tsatsonta 'yar Najeriya ce.

Markel ta bayyana hakan ne a cikin sabon shirinta na Podcast mai taken Archetypes, sashin Hausa na BBC ya rahoto.

Meghan Markle
Kusan Rabin Tsatsona Daga Najeriya ne, Matar ‘Dan Sarki Charles ta Bayyana Babbar Sirrinta Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

Yayin da take zantawa da wata Ba'amurkiya yar asalin Najeriya mai suna Ziwe Fumudoh, matar Yarima Harry ta ce a shekaru da suka gabata ta yi gwajin kwayar halitta wanda ya nuna cewa tana dauke da jinin Najeriya a jikinta har kaso 43 cikin dari.

Kara karanta wannan

An Samu Jihar Farko a Arewa da ta fara Cin Dukiyar Fetur Bayan Gano Danyen Mai

Ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Na yi gwajin kwayar halittata yan shekaru da suka gabata.”

Da aka tambayeta game da sakamakon gwajin, sai ta ce: “Ni yar Najeriya ce da kaso 43 cikin dari.”

Nigerian Tribune ta rahoto cewa wannan jawabi nata ya baiwa Ziwe mamaki, wacce cike da nishadi tace “Babu ta yadda za a yi haka” sannan ta kara da tambayarta daga kabilar da ta fito a Najeriya.

Ziwa ta tambayeta:

"Da gaske kike? Wannan gagarumin abu ne. Daga Kabilar Ibo, Yarbawa, za mu iya sani?”

Surukar sarkin ta amsa da:

“Zan fara bin diddigin duk wadannan abubuwan saboda duk wanda na fadama hakan, musamman matan Najeriya, sai su dunga cewa, kamar yaya?”

Yayin da Ziwe ke bayyana cewa wannan babban kamu ne ga yan Najeriya, ta zolayi Markel cewa shakka babu ta yi kama da yar Najeriya da goggonta “Ouzo.”

Kara karanta wannan

Har Masu Zundena Kan Kwasar Bola da Nake yi Sun bi Sahu na: Tsohuwa Mai Shekaru 63

Ke Tauraruwa Ce: Makauniyar ‘Yar Najeriya Ta Doke ‘Yan Mata 18, Ta Ci Gasar Kyau a Bidiyo

A wani labari na daban, Favour Rufus, budurwa wacce ta hadu da lalurar makanta tun tana da shekaru 18 a duniya, ta lashe gasar sarauniyar kyau na 2022 da aka yi a birnin Port Harcourt.

A wata hira da sashin BBC Pidgin, Favour ta bayyana cewa idonta na hagu a makance yake kuma tana bukatar ganin likita akai-akai don amfani da daya idon.

Ta kuma ce daya idon nata zai makance idan ta yi kuskure wajen magani. Duk da haka, makantanta bai hana ta ci gaba a rayuwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel