Tsohuwa Ta Aske Gashin Kan Jikanta, Ta Yi Masa Kwal Kobo a Wani Bidiyo

Tsohuwa Ta Aske Gashin Kan Jikanta, Ta Yi Masa Kwal Kobo a Wani Bidiyo

  • Wata tsohuwa ta mai da jikanta mai kan kwal-kwal bayan da aka ba ta ajiyarsa, mahaifiyarsa ta tafi makaranta
  • Wani bidiyon da aka yada ya nuna lokacin da yaron ke da gashinsa, daga baya kuma gashinan babu komai a kansa
  • Mahaifiyar ta jijjiga, amma duk da haka ta saduda, mutane da dama sun yi martani mai zafi kan wannan lamari

Wata matar da ta bar danta ga kakarsa ta dawo ta ga abin mamaki yayin da ta ga yadda aka yi masa askin kwal-wal.

Haihxx ta yada wani bidiyo mai daukar hankali a TikTok, tare da cewa ta tafi jami'a ne kuma ta bar yaron domin kakarsa ta kula dashi.

Bidiyon yadda tsohuwa ta aske kan jikanta kwal-kwal ya jawo cece-kuce
Tsohuwa Ta Aske Gashin Kan Jikanta, Ta Yi Masa Kwal Kobo a Wani Bidiyo | Hoto: TikTok/@haihxx
Asali: UGC

A cewartsa, danta na da tarin gashi tun na haihuwa, kuma ta yada bidiyon lokacin da yake da gashinsa cikakke.

Kara karanta wannan

A kirga lafiya: Bidiyon mutumin da yazo siyan kaya da jaka cike da 'yan N10 ya tada kura

Sai dai, tara gashin nan dai bai yiwa tsohuwa kyau ba, don haka ta kame yaro ta kwalkwale kansa tas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin Haihxx game da aikin da aka yi ma danta

Yayin da ta dawo gida ta ga danta da kai kamar kwarya, sai bakin ciki ya kama ta.

Ta rubuta cewa:

"Har yanzu zuciyata na kuna. Kawai dariya na iya yi, mahaifiya ta ce, gashi kuma zai sake tsirowa."

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

@renzomama87 tace:

"Da nine da mun ta fada, domin kuwa ta tsallaka manyan layuka!!!"

@lovelypeaches tace:

"Da nine da na yi matukar fusata."

@ashhbabyy_ tace:

"Gashin zai tsiro daga baya amma dai na rasa me zai sa ta yi mas ahaka ba tare da izininki ba duk kuwa darajarta gareshi."

@K Lee tace:

Da nine ba za mu sake magana ba har abada."

Kara karanta wannan

Ba a cire rai: Budurwa ta ba da mamaki, duk da faduwa a JAMB ta sau 7, ta kammata digiri

@Johnny bravo yace:

"Ban gane a ina kuma don me tsofaffi ke yin haka ba."

Mai Kula da Shago ta Fusata Yayin da Mai Sayen Kaya Yazo da Jaka Makare da 'Yan N10

A wani labarin, Ochulo, wanda aka fi sani da Odogwu Ten Five ya yada wani bidiyon yadda ya je shagon siyan kayan alatu domin sayen wani abun.

Sai dai, kudaden da ya bayar a shagon siyayyan sun jawo rikici tsakaninsa da budurwa mai kula da shagon, wacce ta shiga mamakin ganinsa da irin kudin.

A gajeren bidiyon da ya yada, an ga lokacin Ochulo ya bude jakarsa makare da 'yan Naira goma-goma sannan ya nemi budurwar da ta kirga su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel