An Dakata da Aikin Titin Abuja-Kano Saboda Rashin Tsaro Inji Gwamnatin Najeriya

An Dakata da Aikin Titin Abuja-Kano Saboda Rashin Tsaro Inji Gwamnatin Najeriya

  • Aikin gina titin Abuja-Kaduna-Kano ya tsaya a sakamakon matsalar rashin tsaro da ake fama da ita
  • Karamin Ministan ayyuka da gidaje ya yi wannan bayani yayin da ya je wani ziyarar aiki a Kaduna
  • Umar Ibrahim El-Yakub yace aikin yana tafiya ta bangaren Kaduna da Kano, ana sa ran a gama a lokaci

Abuja - Gwamnatin tarayya tace gyaran hanyar Abuja-Kaduna-Kano da ake yi ya tsaya a dalilin barazanar da ake fuskanta na rashin tsaro a yankin.

Daily Trust ta rahoto karamin Ministan ayyuka da gidaje, Umar Ibrahim El-Yakub yana mai wannan bayani yayin da ya duba wani aikin titi a Kaduna.

Hon. Umar Ibrahim El-Yakub yace an tsaida aikin bayan harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja-Kaduna a watan Maris, aka yi gaba da wasu fasinjoji.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Rahoton yace Ministan ya fitar da jawabi a karshen makon da ya gabata ta bakin Darektansa na yada labarai da hulda da jama’a, Blessing Lere-Adams.

Ba a tsaida aikin cak ba

Blessing Lere-Adams tace akasin abin da mutane ke fada cewa an yi watsi da aikin, ba haka lamarin yake ba, an dakata da aikin ne kuma za a cigaba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Darektar ma’aikar ayyuka da gidajen tace ba da dadewa ba za a cigaba da aikin wannan titi na Abuja-Kaduna-Kano domin an samu tsaro a yanzu.

Titin Abuja-Kano
Titin Abuja-Kano Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Ministan ya kuma bayyana cewa aikin yana cigaba da tafiya a sauran bangarorin titin.

A cewar Umar Ibrahim El-Yakub, aikin ya kai matakin da za a yaba, ya tabbatar da cewa ‘yan kwangila za su kammala ginin titin a lokacin da aka tsara.

"Muna sa ran bangare na biyu da na uku na hanyar za su kammala daga yanzu zuwa farkon shekarar badi.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Sanata da Gwamnan APC Ya Shiga Uku, An Rufe Shi a Gidan Yari

Amma bangare na farko zai dauki fiye da wannan lokaci, saboda dalilan da sun bayyana a zahiri.
'Dan kwangila yana aiki a sauran bangarorin hanyar a lokaci daya kafin 'yan ta'adda su kai harin jirgin kasa
Kuma an yi fiye da 50% na aikin a sashen farko kafin ‘dan kwangilar ya tsaida aiki saboda rashin tsaro."

- Karamin Ministan ayyuka da gidaje

ISWAP sun kashe Boko Haram

A ranar Lahadin da ta gabata kuka ji labari cewa mayakan ISWAP sun dura mafakar ‘yan Boko Haram, kuma sun hallaka ‘yan ta’addan a jihar Borno.

Sojojin ISWAP sun rutsa ‘Yan Boko Haram, sun kashe shida daga cikinsu, sannan sun dauke makamansu a rikicin cikin gidan da suka saba tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel