Borno: An yi Mummunar Arangama Tsakanin Mayakan ISWAP da Boko Haram, An Halaka 6

Borno: An yi Mummunar Arangama Tsakanin Mayakan ISWAP da Boko Haram, An Halaka 6

  • Mummunan yaki ya barke tsakanin mayakan ta’addancin ISWAP da na Boko Haram a garin Gajibo dake da nisan kilomita 95 daga birnin Maiduguri
  • A farmakin da ‘yan ISWAP suka kai kan ‘yan Boko Haram din, sun halaka 6 daga ciki inda suka kira su da kafirai
  • Zagazola Makama ya bayyana cewa, wannan mummunan arangamar na iya zama babban kalubale ga kungiyoyi ta’addancin abokan hamayyar juna

Borno - A wani abinda yayi kama da cigaban arangama tsakanin kungiyoyin ta’addanci masu hamayya da juna, mayakan ta’addancin ISWAP sun kai mummunan farmaki maboyar Boko Haram a cikin kwanakin karshen mako inda suka halaka mutane shida har lahira.

Taswirar Borno
Borno: An yi Mummunar Arangama Tsakanin Mayakan ISWAP da Boko Haram, An Halaka 6. Hoto daga TheCable.com
Asali: UGC

A wani aikin sirri da ‘yan ta’addan ISWAP suka yi, sun dira gidajen ‘yan ta’addan Boko Haram a Gajibo, gari ne nisan kilomita 95 arewa maso gabashin Maiduguri, babban birnin jihar Borno kuma suka yanka mutum shida da suka ayyana da kafirai.

Kara karanta wannan

Borno: Sojojin Najeriya Sun Halaka ‘Yan Ta’adda 31, Sun Damke 70 a Borno

Wata majiyar sirri ta sanar da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ta’addanci da kiyasi kan tsaro a tafkin Chadi, cewa maharan sun samo bindigu kirar AK 47 guda biyar daga ‘yan Boko Haram.

ISWAP sun kai manyan farmaki cike da nasara kan ‘yan ta’addan Boko Haram a sakamakon rikicin dake tsakaninsu wanda ya janyowa kungiyar mummunan asarar rayuka da kadarori.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cigaban rikici tsakanin kungiyoyin hamayyar, zai iya janyo miyagun barna saboda ‘yan ISWAP sun sha alwashin yakar tsoffin mambobinsu fiye da dakarun soji.

Yan Bindiga Sun Sheke Fasinjoji 2, Sun Yi Garkuwa da Wasu 3 a Katsina

A wani labari na daban, a daren Asabar ne fasinjoji biyu suka rasa rayukansu inda aka yi garkuwa da wasu ukun bayan tawagar ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai suka mai hari iyakar Magamar Jibia dake karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji Sun Ragargaza Fitaccen Shugaban ‘Yan Bindiga Zamfara, Chire

Wani ganau wanda ya bukaci a boye sunansa ya sanar da Channels TV a ranar Lahadi cewa ‘yan bindigan sun kai farmakin wurin karfe 9:15 na dare.

Ya bayyana cewa tawagar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji sun fatattake su bayan tsare ababen hawan biyu da suka yi a babban titin tare da kashe fasinjoji tare da garkuwa da wasu uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel