'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dan Fitaccen Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dan Fitaccen Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto

  • Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne sun kashe Ɗan banga a kauyen Rimawa, karamar hukumar Goronyo a jihar Sakkwato
  • Maharan sun kuma jikkata wani mutum ɗaya kana suka yi awon gaba da ɗan mamba mai wakiltar Goronyo a majalisar dokokin jihar
  • Mamban majalisar, Faruk Ahmadu Rimawa, yace maharan sun kira waya amma har yanzun ba su nemi komai ba

Sokoto - Wasu yan bindiga da ake zaton 'yan fashin daji ne sun halaka wani ɗan Banga, Malam Bakwai, a ƙauyen Rimawa, ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto.

Maharan sun kuma jikkata wani mutum ɗaya daga bisani suka yi awon gaba da ɗan mamba mai wakiltar mazaɓar Goronyo a majalisar dokokin jihar Sakkwato.

Yan bindiga a Sakkwato.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dan Fitaccen Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin ya auku ne da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba, 2022.

Kara karanta wannan

'Ƴan Bindiga Sun Halaka Babban Jami'in Tsaro Da Hadimansa Biyu a Wata Jihar Najeriya

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, shugaban ƙaramar hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, yace 'yan bindigan sun kai faramaki kauyan da karfe 4:00 na yamma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, maharan sun shiga ƙauyen a kan Babura daban-daban kuma kowane ɗaya na ɗauke da 'yan bindiga uku.

"Ni da shugaban jam'iyyar PDP na jiha mun je garin Goronyo domin yin ta'aziyya yayin da aka sanar da ni game da harin. Na yi gaggawar haɗa jami'an tsaro zuwa kauyen amma sun tafi da yaron tun kafin mu isa."
"Bayan haka sun kashe wani ɗan Banga ɗaya sannan kuma suka jikkata wani mutum ɗaya."

Wane hali iyalan ɗan majalisar ke ciki?

Legit.ng Hausa ta gano cewa yaron ɗan majalisar ya je ƙauyen ne tare da mahaifiyarsa amma ita ta tsira ba tare da jin rauni ba.

Kara karanta wannan

An Samu Sabon Cigaba da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Jam'iyyar PDP Ta Ɗage Yakin Neman Zaɓe

Ɗan majalisar, Faruk Ahmadu Rimawa, yace masu garkuwan sun kira waya amma har yanzun ba su faɗi abinda suke buƙata ba.

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya Sun Dakile Harin Kwantan Bauna da Boko Haram Suka kai Musu, Sun yi Musu Lugude

Mayakan ta’addancin Boko Haram sun dasawa sojojin dake wucewa bam duk a cikin harin kwantan bauna a Borno.

Sai dai reshe ya juye da mujiya yayin da sojojin suka dakile harin tare da far wa ‘yan ta’addan inda suka budewa ‘yan ta’addan wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel