'Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Jami'an Tsaron AVG Na Jihar Anambra

'Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Jami'an Tsaron AVG Na Jihar Anambra

  • Wasu yan bindiga sun kashe wani babban ɗan Banga da wasu mutum biyu dake ba shi tsaro a yakin Aguata jihar Anambra
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun buɗe wa yan bangan Uku wuta a wata Kasuwa a Igboukwu, nan take suka mutu baki ɗaya
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mr Tochukwu Ikenga, yace tuni dakaru suka tsananta bincike don kamo maharan

Anambra - Wasu Miyagun Yan bindiga da ake kyautata zaton makasa ne sun kashe jami'an ƙungiyar 'Yan bangan Jihar Anambra (AVG) a kauyen Igboukwu, ƙaramar hukumar Aguata.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa waɗanda aka kashe ɗin sun haɗa da, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar wanda aka fi sani da Shaba da kuma wasu biyu dake tare da shi.

Hari a jihar Anambra.
'Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Jami'an Tsaron AVG Na Jihar Anambra Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

A cewar wata majiya, yan Bangan na wurin wata mashaya a fitacciyar kasuwar Nkwo da ke garin Igboukwu lokacin da yan bindigan suka buɗe musu wuta.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: An Gano Wani Bawan Allah Tsirara da Aka Kulle Tsawon Shekara 20 a Kaduna

Majiyar ta ƙara da cewa maharan sun isa wurin a cikin abin hawa, tun daga kan Motar suka buɗe wa Yan bangan biyu wuta a kofar shiga wurin kafin daga bisani su kutsa ciki su bindige babban jami'in har lahira.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahotanni sun ce nan take mutanen suka mutu, har yanzu babu cikakken bayani kan musabbabin kashe yan bangan.

Sai wani rahoto ya nuna Shaba, babban Ɗan Banga a kauyen, yana cikin ƙungiyar da ake tsoro, Ebubeagu security group, wacce ke ta da zaune tsaye a yankunan kudu maso gabas, musamman jihohin Ebonyi da Imo.

Wata majiyar ta daban ta yi ikirarin cewa wata tawagar masu garkuwa ne suka ƙashe jami'an tsaron bayan Shaba da tawagarsa sun fasa shugabansu a wasu kwanaki da suka gabata.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mr Tochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da lamarin yace an tsaurara matakan tsaro a yankin yayin da dakaru suka bazama don kamo maharan.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Wani Matashi Ya Naushi Abokinsa, Ya Faɗi Ya Mutu a Birnin Kano

"Yanzu haka dakaru na kan aiki don kamo maharan, an kara tsananta Sintiri a yankin Aguata da kewaye, zamu sanar da duk wani ci gaba da aka samu," Inji shi.

A wani labarin kuma Bayanai Sun Fito Kan Rahoton Dake Yawo Wasu Matasa Sun Farmaki Ayarin Bola Tinubu Na APC

Hukumar yan sandan jihar Osun ta musanta wani rahoto da ake yaɗa cewa cewa wasu matasa sun farmaki Bola Ahmed Tinubu.

Kwamishinan yan sandan jihar, Olawale Olokode, yace Bidiyon da ake yaɗa ba na yanzu bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel