Da Dumi-duminsa: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Basarake A Wata Jihar Arewa

Da Dumi-duminsa: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Basarake A Wata Jihar Arewa

  • Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da hakimin kauyen Iyaka da ke masarautar Gummi a jihar Zamfara
  • Maharan sun farmaki kauyen ne da misalin karfe 1:45 na ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba bayan sun ajiye baburansu a jeji
  • Yan bindigar sun kuma kai hari kauyen Msama-Mudi da ke makwabtaka da karamar hukumar Bukkuyum inda suka sace masu jego 8 da matasa hudu

Zamfara - Wasu guggun yan bindiga sun yi garkuwa da hakimin kauyen Iyaka da ke masarautar Gummi a jihar Zamfara a ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba, HumAngle ta rahoto.

An sace hakimin mai suna Marafa Danbaba da misalin karfe 1:45 na rana a gidansa da ke karamar hukumar Gummi bayan sun farmaki kauyen.

Kara karanta wannan

2023: Kusoshin Kiristocin Jam’iyya Za Su yi Taron Dangi Domin Dankara Tinubu da Kasa

A cewar wasu da abun ya faru kan idanunsu, maharani sun ajiye baburansu a cikin jeji kafin suka taka zuwa kauyen sannan suka farmaki gidansa.

Yan bindiga
Da Dumi-duminsa: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Basarake A Wata Jihar Arewa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Matsalar rashin tsaro a Zamfara na ci gaba duk da agajin da rundunonin tsaro ke kaiwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Asabar, an sake kai wani hari a kauyen Msama-Mudi da ke makwabtaka da karamar hukumar Bukkuyum.

A yayin farmakin, maharan sun nemi wani manomi da suka samu yana hutawa a karkashin bishiya da ya nuna masu gidajen masu kudi a garin.

Wani malamin makaranta mai suna Mustapha Mamman yace:

“Yan ta’addan sun tursasa Lauwali Dan-tawasa nuna masu gidajen masu kudi a kauyen. Amma ya fada masu cewa bai san su ba. Hakan da yayi yasa sun sace dansa.”

Sauran mutanen da aka sace a harin sun hada da masu jego takwas da wasu matasa maza su hudu.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Rikakkun Kwamandojin ‘Yan Bindiga 5 da Suka fi Bello Turji Hatsari a Zamfara

A cewar Musa Isah Masama, an ajiye jinjiri dan wata biyar a kasa yayin da aka sace mahaifiyarsa.

Surukin hakimin da aka sace a ranar Lahadi, Ibrahim Aminu ya ce sun lura da yawan sa ido.

Jagoran karamar hukumar Gummi, Abubakar Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin a Iyaka yana mai cewa zuciyarsa tayi nauyi da samun mummunan labarin.

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Matasan Jam'iyyar APC a Wata Jiha

A wani labarin, mun ji cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Hon. Lucky Okechukwu, shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Igboeze ta kudu da ke jihar Enugu, rahoton Sahara Reporters.

Koda dai babu cikakken bayani kan lamarin, an tattaro cewa an harbe Okechukwu ne har lahira a daren ranar Asabar, 8 ga watan Oktoba a garin Unadu.

Wani jigon jam’iyyar a jihar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a bashi umurnin magana ba, ya tabbatar da faruwar lamarin, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Mata da Yara 30 Sun Yi Shahada, Sun Nutse a Ruwa Za Su Tserewa ‘Yan Bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel