Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Matasan Jam'iyyar APC a Wata Jiha

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Matasan Jam'iyyar APC a Wata Jiha

  • Tsagerun 'yan bindiga sun bindige Hon. Lucky Okechukwu, shugaban matasan jam’iyyar APC a karamar hukumar Igboeze ta kudu da ke jihar Enugu
  • An tattaro cewa maharan sun farmaki marigayin ne a daren ranar Asabar, 8 ga watan Oktoba
  • Rundunar yan sandan jihar bata fitar da jawabi kan lamarin ba amma wani jigon APC ya tabbatar da lamarin

Enugu - Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Hon. Lucky Okechukwu, shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Igboeze ta kudu da ke jihar Enugu, rahoton Sahara Reporters.

Koda dai babu cikakken bayani kan lamarin, an tattaro cewa an harbe Okechukwu ne har lahira a daren ranar Asabar, 8 ga watan Oktoba a garin Unadu.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari, Sun Kashe Mai Anguwa da Wasu Mutune a Jihar Arewa

Yan bindiga
Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Halaka Shugaban Matasan Jam'iyyar APC Mai Mulki Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani jigon jam’iyyar a jihar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a bashi umurnin magana ba, ya tabbatar da faruwar lamarin, rahoton Punch.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Eh, da gaske ne. ban san ainahin sunansa ba amma mun samu labarin cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe shi a daren jiya. Idan jam’iyyar na son magana kan lamarin, lallai za ta saki jawabi kan haka.”

Yan sanda basu rigada sun tabbatar da lamarin ba kuma kakakin yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe, bai amsa kira da sakon tes ba, Sahara Reporters ta ruwaito.

Yadda Matar Malamin Addini, Yaransa 2 Da Kanne Mata 2 Suka Yi Mutuwar Ban Mamaki

A wani labarin, mun ji cewa an tsinci matar wani malamin addini mai suna Adolphus Odo kwance a mace tare da yaranta biyu da kuma kannenta biyu a Amutenyi, da ke Obollo-Afor, karamar hukumar Udenu ta jihar Enugu a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

'A Soke EFCC,' Matasan Ibadan Suka Fada Wa FG, Sun Yi Babban Zanga-Zanga

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa karar kararrawar agogo ce ta ankarar da makwabta inda suka fasa kofar kawai sai suka tsinci mutanen su biyar kwance babu rai a jikinsu.

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban karamar hukumar, Solomon Onah, ya ce labarin ya jefa yankin karamar hukumar cikin alhini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel