Jerin Sunaye: Rikakkun Kwamandojin ‘Yan Bindiga 5 da Suka fi Bello Turji Hatsari a Zamfara

Jerin Sunaye: Rikakkun Kwamandojin ‘Yan Bindiga 5 da Suka fi Bello Turji Hatsari a Zamfara

  • Duk da fice tare da shaharar Bello Turji a matsayinsa na gogarman 'dan bindiga, akwai wasu 'yan bindiga da suka fi shi hatsari a jihar Zamfara
  • Daga cikin mashahuran 'yan bindigan akwai Ado Aleru, Dan Ngala, Shadari, Halilu Buzu da Dogo Gudale wadanda barnarsu ta zarce ta Turji
  • An gano cewa, sune wadanda suka jagoranci kai farmkain Jangebe, Tegina da sauransu kuma sun addabi hatta jihohi maus kusanci da Zamfara

Zamfara - Bello Turji mashahurin ‘dan bindiga ne da ya addabi yankuna da yawa na jihar Zamfara. Sai dai duk da shahararsa, kiyasi a kan tsaro wanda Zagazola Makama ya bayyana ya lissafo wasu kwamandojin ‘yan bindiga biyar da suka fi Bello Turji hatsari da shu’umanci a jihar Zamfara.

Kaduna
Jerin Sunaye: Rikakkun Kwamandojin ‘Yan Bindiga 5 da Suka fi Bello Turji Hatsari a Zamfara
Asali: UGC

Ga jerin sunayensu da bayanai:

1. Ado Aleru

Kara karanta wannan

Mata da Yara 30 Sun Yi Shahada, Sun Nutse a Ruwa Za Su Tserewa ‘Yan Bindiga

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Aleru na zama ne a Munhaye dake karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara kuma shi ne da alhakin hare-hare masu yawa a kananan hukumomin Tsafe da Gusau.

Suna addabar jihohi masu makwabtaka kamar Katsina tare da manyan hanyoyin Gusau zuwa Funtua.

2. Dan Nagala

Sansanin Dan Nagala yana nan a yankin Bozaya Mai Rai dake sakin Gandu dake hade kananan hukumomin Maru- Anka da Talata Mafara.

Shi ke da alhakin kai manyan hare-hare a kauyukan Maru, Talata Mafara, Bungudu da Maradun kuma suka sace ‘yan makarantar Tegina da na Jangebe tare da ajiye su a sansanoninsu.

3. Shadari

Shadari yana zama a sakin Gandu a kusa da iyakar Maru da Anka. Shi ke da alhakin kai miyagun farmaki a kananan hukumomin Anka, Bukkuyum, Bakura da Gummi tare da jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari, Sun Kashe Mai Anguwa da Wasu Mutune a Jihar Arewa

4. Halilu Buzu

Halilu Buzu da babban abokinsa Umaru Nagona an gano sun koma dajin Magiri kusa da iyakar Maru da Anka a farkon daminar bana.

Shi ke da alhakin kai farmaki a Anka, Talata Mafara, Bakura da jihar Sokoto.

5. Dogo Gudale

Gudale yana rayuwa a dajin Fasa Gora dake karamar hukumar Bukkuyum. Shi ke da alhakin kai hare-hare a Bukkuyum da Gummi tare da kauyuka masu makwabtaka da jihohi Sokoto da Kebbi.

Bidiyon Turnukun Yaki Tsakanin Boko Haram da ISWAP, ‘Yan Boko Haram 8 Sun Sheka Lahira

A wani labari na daban, mayakan ta’addanci na ISWAP sun halaka mayaka takwas na kungiyar ta’addancin Boko Haram a wata arangama da suka yi a Borno.

ISWAP tsagi ne ba kungiyar ta’addancin Boko Haram kuma sun rabe ne sakamakon rikicin shugabanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel