Gwamnati Tayi Maganar Biyan Kudi a Ceto Ragowar Fasinjojin Jirgin Abuja-Kaduna

Gwamnati Tayi Maganar Biyan Kudi a Ceto Ragowar Fasinjojin Jirgin Abuja-Kaduna

Mua’zu Jaji Sambo yace ba a biya kudi domin a fanshi fasinjojin jirgin da ‘yan ta’adda suka dauke ba

Ministan sufurin tarayya ya yi wannan karin haske ne yayin da ya tattauna da wasu ‘yan jarida a Abuja

Tun da babu wani wanda yake hannun ‘yan ta’adda a yanzu, Injiniya Sambo yace jirgin zai cigaba da aiki

Abuja - Ministan sufuri na kasa, Mua’zu Jaji Sambo yace ba a biya kudi domin fansar ragowar fasinjojin Kaduna zuwa Abuja da aka yi garkuwa da su ba.

Daily Trust tace Ministan ya yi wannan bayani a lokacin da ya zanta da wasu manema labarai a garin Abuja a ranar Juma’a, 7 ga watan Oktoba, 2022.

Injiniya Mua’zu Jaji Sambo yace duk da an sasanta wajen kubutar da wadannan mutane, amma babu sisin kobon gwamnati da ya yi cikas a dalilin haka.

Kara karanta wannan

Yadda Hadimin Gumi ya Dinga Tarwatsa Kokarin FG na Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa, Jami’i

Zaman Gwamnati da 'yanuwan fasinjoji

Da yake bayanin abin da ya faru, Mai girma Ministan tarayyan yace yana shiga ofis ya yi kokarin zama da iyalan fasinjojin nan da aka yi garkuwa da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A lokacin da ya hadu da ‘yanuwan wadannan Bayin Allah a watan Agusta ne ya shaida masu gwamnati tana abin da ya dace domin a ceto fasinjojin.

Ministan sufuri
Sabon Ministan sufuri, Muazu Sambo Jabi Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Jaridar ta rahoto Muazu Jaji yace ya fadawa ‘yanuwan wadanda aka sace su ba jami’an tsaro hadin-kai domin a iya dawo da mutanen da aka yi gaba da su.

A karshe dai an yi dace, duk ragowar fasinjojin da aka yi garkuwa da su sun dawo gidajensu, wannan karo Ministan yace ba a biya ‘yan ta’addan wani kudi ba.

Za a cigaba da aiki da jiragen kasa

Tun da babu wanda ya rage yanzu a hannun ‘yan ta’addan, Ministan sufurin yace NRC za ta dawo da daukar fasinjoji kamar yadda aka saba ta jiragen kasan.

Kara karanta wannan

Matasan Yara 3 Sun Arce Daga Hannun ‘Yan Bindiga Yayin da Bacci Yayi Awon Gaba da Miyagun

“Watanni shida da kwanaki bakwai kenan da aka dakatar da aikin jirgin kasa a wannan hanya.
Kuma ya kamata in sanar da ku cewa Injiniyoyinmu na gida na kamfanin NRC ne suka yi aikin gyara da sake gina dogon da ya lalace

- Muazu Sambo Jaji

Mutane 23 sun dawo gida

Kun ji labari sauran mutane da aka dauke a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna tun a watan Maris ba su hadu da iyalansu ba, sai bayan kubutar da su a makon nan.

Kamar yadda Dr. Yusuf Usman ya bayyanawa Duniya, da kimanin karfe 4:00 na yammacin ranar Laraba aka ceto sauran fasinjojin da suka yi kwana 191 a daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel