Matasan Yara 3 Sun Arce Daga Hannun ‘Yan Bindiga Yayin da Bacci Yayi Awon Gaba da Miyagun

Matasan Yara 3 Sun Arce Daga Hannun ‘Yan Bindiga Yayin da Bacci Yayi Awon Gaba da Miyagun

  • Matasan yara 3 na Fulani da ‘yan bindiga suka sace sun tsere daga hannun miyagun bayan bacci ya kwashe masu gadinsu
  • An gano cewa ‘yan bindiga sun kutsa kauyen Fulanin tare da yin garkuwa da yaran kuma suka bukaci kudin fansa N100 miliyan
  • Ba a daure matasan yaran ba, hakan yasa suka arce zuwa kauyensu na Gwanda dake gundumar Gurdi a Abaji

FCT, Abuja - Matasan yaran Fulani uku da ‘yan bindiga suka yi garkuwa dasu a Gwamna dake gundumar Gurdi dake yankin Abaji a Abuja sun sha da kyar bayan wadanda suka sace su sun yi bacci.

Gunmen
Matasan Yara 3 Sun Arce Daga Hannun ‘Yan Bindiga Yayin da Bacci Yayi Awon Gaba da Miyagun. Hoto daga Channelstv
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna tana da kusan nisan kilomita daga kauyen Gulida dake yankin.

Kara karanta wannan

Sojinmu Gwaraza ne, Babu Aikin da Ba Zasu Iya ba: Buhari Yana Murnar Dawowar Fasinjojin Jirgin Kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kansilan dake wakiltar gundumar Gurdi, Wozhe Ishaya, wanda ya tabbatar da tserowar yaran ga Daily atria a waya a ranar Alhamis, yace wadanda aka sacen sun kubuta a daren Talata.

Yace ‘yan bindigan sun kutsa yankin Fulanin wurin karfe 11 na dare kuma suka yi awon gaba da yaran maza masu shekaru 12, 14 da 16.

“Amma kamar yadda Ubangiji yaso, ‘yan bindigan sun yi bacci kuma basu kulle yaran ba hakan yasa suka tsere hankali kwance zuwa kauyen Gwanda.”

- Yace.

Yace ‘yan bindigan sun kwashe wasu raguna zuwa sansaninsu kuma sun yanka su.

Hakimin Gulida, Abubakar Sadauna, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya koka da yadda farmakin ‘yan bindiga ya addabi yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar babban birnin tarayya, DSP Adeh Josephine har yanzu bai yi martani kan sakon kar ta kwana da aka tura masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel