Yadda Hadimin Gumi ya Dinga Tarwatsa Kokarin FG na Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa

Yadda Hadimin Gumi ya Dinga Tarwatsa Kokarin FG na Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa

  • Mamba a kwamitin fadar shugaban kasa na ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, Atta Abdulmalik ya sanar da ta’asar da Tukur Mamu ya dinga tafkawa
  • Atta yace tun farko ‘yan ta’addan basu bukaci kudi daga hannun kowa ba, Mamu ne ya shiga ya fita tare da zagon kasa ga kokarin gwamnatin tarayya
  • Ya bayyana yadda kwamitin ya shiga daji, suka kwana tare da sadaukar da rayuwarsu kuma har suka tattauna da ‘yan ta’addan

FCT, Abuja - Dr Abdulmalik Atta, mamban kwamitin shugaban kasa da ya assasa ceto ragowar fasinjoji 23 da aka yi garkuwa dasu a farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris, ya zargi Tukur Mamu da zagon kasa ga kokarin ceto wadanda aka sace.

Kara karanta wannan

Biliyoyin da Shugabanni Suka Wawure Daga Najeriya Suna Dankare a Turai, Buhari

Atta wanda mahaifinsa ya daga cikin fasinjojin da aka sace, yayi wannan ikirarin ne a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels.

Tukur Mamu
Yadda Hadimin Gumi ya Dinga Tarwatsa Kokarin FG na Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atta yace Mamu yayi duk wani abinda zai iya domin tarwatsa kokarin gwamnatin tarayya na ceto wadanda aka sace don wani buri nasa.

Yace:

“Saboda Mamu ya kawo kudi cikin lamarin ceto fasinjojin, iyalan wadanda lamarin ya ritsa dasu, sun yi asarar $200,000 kafin shigar shugaban ma’aikatan tsaro lamarin.
“Kwamitin fadar shugaban kasan ya fuskanci manyan kalubale yayin da muka shiga dajika domin ganawa da ‘yan bindiga har da kwana.
“Wata shida kenan da mako daya ana mun godewa Ubangiji kan yadda komai yazo karshe a yanzu. Muna godiya ga goyon bayan gwamnatin tarayya ta ofishin shugaban ma’aikatan tsaro. Mun shiga daji kuma mu kwaso sauran iyalanmu.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutu Ranar Litinin Don Murnar Eid-l-Maulud

Ya kara da cewa:

“Mun samu wannan nasarar ne ba ta hannun wani wanda ya ci amanar kwamitin da gwamnati, ina magana ne kan Tukur Mamu wanda yayi duk yadda zai iya wurin dakile kokarin gwamnati. Kamar yadda muka sani, yana hannun gwamnati yanzu. Amma mun godewa Ubangiji, dukkan iyalanmu sun dawo.
“‘Yan bindigan basu tambaya kudi ba tun farko, Tukur Mamu ne ya shigo da batun kudi kuma ya lalata komai na tsawon wata shida.
“Mun kwashe kusan 200,000 na dalar Amurka. Muna godiya ga Ubangiji CDS da kansa ya dauka nauyin kuma kwamitin bai taba tambayar ko kobo ba. Duk wani sadaukarwa da aka yi na kai ne.
“A kwamitin, zan iya tabbatar muku cewa nayi aiki da mutane masu matukar kwazo. Da ina da dama da dukkansu na basu lambar yabon kasa. Mun sadaukar da rayukanmu, Mun je daji har mun kwana.
“Mun saurari korafin ‘yan ta’addan duk da mun san basu kyauta ba a bai da suka yi amma sai da muka tattauna.

Kara karanta wannan

Ka yi abin kirki: CAN ta ji dadi, ta yabawa Buhari bisa ceto fasinjojin jirgin Abj-Kad

“Gaba-gaba zuwa hukumomin tsaronmu, dole su bada karfi wurin irin wannan aikin kuma su dinga tattaunawa da su.”

DSS Ta Kama Mahaifin Matar Tukur Mamu A Yayin Da Ake Fadada Bincike

A wani labari na daban, 'yan sandan farin kaya na DSS na cigaba da bibiyan wadanda ke da alaka da Tukur Mamu, wanda ya taimaka wurin sulhu da yan bindiga, a yayin da suka kama surukinsa, Abdullahi Mashi, a daren ranar Alhamis.

Daily Trust ta tattaro cewa jami'an yan sandan sirrin sun kuma ziyarci gidan surukin Mamu, Ibrahim Tinja, wanda shima an kama shi an kuma dawo da shi Najeriya tare da mawallafin na Desert Herald a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel