Yajin Aiki: Abinda Muka Tattauna da Shugaba Buhari Kan ASUU, Gbajabiamila

Yajin Aiki: Abinda Muka Tattauna da Shugaba Buhari Kan ASUU, Gbajabiamila

  • A ranar Talata, shugabannin majalisar dokokin tarayya suka gana da shugaba Buhari kan yajin aikin ƙungiyar Malaman jami'o'i
  • Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa taron ya yi armashi kuma zasu sake koma wa ranar Alhamis
  • Yace shugagan kasa ya ji daɗi kuma ya karbi rahoto da shawarwari domin yin nazari a kai gabanin yanke hukunci na ƙarshe

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da shugabannin majalisar wakilan tarayya kan yajin aikin Malaman Jami'o'i ranar Talata a fadarsa.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito cewa kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ne ya jagoranci tawagar majalisar zuwa wurin shugaban ƙasa.

Kakakin majalisar dokokin tarayya, Femi Gbajabiamila.
Yajin Aiki: Abinda Muka Tattauna da Shugaba Buhari Kan ASUU, Gbajabiamila Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake zantawa da yan jaridar gidan gwamnati jim kaɗan bayna kammala taron, Gbajabiamila, ya bayyana cewa taron da suka yi da shugaban ƙasan ya yi kyau sosai, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

ASUU Bata Da Wasu Dalilai Masu Kwari Na Ci Gaba Da Yajin Aiki - Buhari

Yace shugaba Buhari ya amince zai yi nazari kan shawarin majalisar waɗanda suka ta'allaƙa kan yadda za'a kawo ƙarshen yajin aikin Malaman jami'o'i kusan watanni takwas kenan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Shugaban ƙasa kamar yadda aka saba yana da kunnen sauraro, ya karɓi rahoton mu ya ji daɗi kuma ya amince da shi. Mun tattauna sosai kuma dalla-dalla kan abinda rahoton ya ƙunsa."
"Yana son ya duba da kansa. Zamu sake zama ranar Alhamis tsakanin mu da shugaban ƙasa domin jin hukuncin da ya yanke na ƙarshe."

- Femi Gbajabiamila.

Me rahoton ya ƙunsa?

Kakakin majalisar tarayya ya ƙara da cewa rahoton da suka miƙa wa shugaban ƙasa ya kunshi sakamakon jerrin tarukan da suka gudanar da masu ruwa tsaki a ɓangaren ilimin ƙasar nan.

A cewar Mista Gbajabiamila, Buhari ya amince zai duba rahoton kuma ya nemi lokaci domin ya bi ko ina ya duba sannan bayan haka zai ɗauki mataki na karshe ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari

Shugaban majalisar ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba wannan yajin aikin da ASUU ta kafe a kai zai zo ƙarshe domin kowane ɓangare ya amince a sasanta domin ƙasa.

Jagororin majalisar dokokin tarayya sun zauna da ASUU da sauran hukumomin gwamnatin tarayya sau biyu a watan Satumba da nufin kawo ƙarshen yajin aikin da ya shafe watanni Bakwai.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta buƙaci kungiyar ASUU ta mutunta umarnin Kotu ta jange yajin aiki

Gwamnatin Tarayya ta ja kunnen Kungiyar Malaman Jami’a akan kin bin dokar Kotun Ma’aikatun Kasa ta Najeriya (NICN) na ta koma kan aikinta daga dogon yajin aikin da ta ke yi.

Chris Ngige , Ministan Kwadago da Ayyuka, ya ce Kungiyar tana kera wa ‘yan Najeriya karya akan batun cikashe fom din daukaka karar akan umarnin kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel