Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arzikin Kasar, Kwankwaso

Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arzikin Kasar, Kwankwaso

  • Sanata Rabiu Kwakwaso ya fara bayyana abubuwan da zai yi idan ya zama shugaban kasar Najeriya
  • Hukumar zabe ta INEC ta bude filin fara yakin neman zabe tun ranar Larabar da ta gabata
  • Rabiu Musa Kwankwaso dai shine ɗan takarar da Jam'iyyar NNPP ta tsayar a Shugaban Ƙasa

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, a ranar Litinin din nan data gabata, ya yi alkawarin habaka tattalin arzikin kasar tare da sake fasalin Nijeriya idan aka mara masa baya a zaben shekarar 2023

Kwankwason ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Jalingo Babban birnin Jihar Taraba, ya kuma yi alkawarin sanya ilimi a matsayin farko a gwamnatinsa, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP Za Ta Kira Taron Gaggawa Domin Ceton Takarar Atiku Daga Watsewa

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya kara da cewa gwamnatinsa za ta samar da yanayi mai kyau ga kananan ‘yan kasuwa ta hanyar bunkasa yanayin kasuwancinsu tare da karfafawa mata da matasa gwuiwa dan damawa dasu aharkokin kasuwanci.

Ya ce,

“Za mu ba da fifiko kan ilimi, zamu magance matsalar rashin tsaro da yanayi mai kyau dan haɓaka kasuwanci”
“Da wadannan matakan zamu samawar da ƴan kasa damarmaki haɗi da bude musu hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Za mu inganta abubuwan da ake samarwa a gida da kuma tsarin shigo da kayayyaki da samar da ayyukan yi A cikin gida. Wadannan da ma wasu da dama su ne batutuwan da zamu maida hanakali a kai.
“Kullum muna tashi mu ga ƙudin kasar nan darajarar sa tayi ƙasa, kullum ƙudin kasashen waje kara hawa yak e. wannan na cikin abun da gwanati ta kamata ta kalla; amma ina, ku duba kuga yadda kullum tattalin arziki ke tabarbarewa”

Kara karanta wannan

Muhimmin Abun Da Zan Yi Idan Na Ɗare Kujerar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 2023, Kwankwaso

Kwankwaso
Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Najeriya, Kwankwaso
Asali: Getty Images

A kan matsayin na sake fasalin kasa, Kwankwaso ya ce zai yi aiki kafada da kafada da Majalisar Dokokin kasa da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, domin fara aikin sake fasalin tun daga tushe.

Ya yi nuni da cewa, tsarin nasa wanda nan ba da dadewa ba za a gabatar da shi ga jama’a, ya yi duba da yanayin da kasar nan ke ciki, tare da mai da hankali kan yadda halin da al’umma suka shiga dangane da harkokin mulki, ya kara da cewa dole ne Najeriya ta dawo da matakan da ta dauka domin daidaita lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel