Kungiyar ASUU Bata Da Wasu Dalilai Masu Kwari Na Ci Gaba Da Yajin Aiki - Buhari

Kungiyar ASUU Bata Da Wasu Dalilai Masu Kwari Na Ci Gaba Da Yajin Aiki - Buhari

  • Har Yanzu an kasa samun Daidato tsakanin ƙungiyar malaman jami'oi da gwamnatin Tarayya
  • Ko a Satin da ya gabata ma dai, Kakakin Majalissar Wakilan tarayya ya yi ƙokarin shiga tsakani
  • Tun Fabairun shekarar damu ke ciki ne dai ƙungiyar ta shiga yajin aikin sai mama ta gani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, da ba a sulhunta da su ba sun kafe ne kan wasu dalilai marasa tushe, kuma suna yunkurin daƙusar da irin ƙwazon da gwamnati ke sawa a fannin ilimi.

Buhari ya bayyana haka ne a wajen taro kan yadda za'a rage cin hanci da rashawa a ma’aikatun gwamnati, mai taken: “Cin hanci da rashawa a fannin ilimi” .

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Rashin Aikin Yi Cikin Matasa Ka Iya Haifar da Tarzoma A Kasa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ICPC tare da hadin gwiwar ofishin sakataren gwamnatin tarayya suka shirya da Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga jami'a, tare da tallafin gidauniyar MacArthur ne suka shirya taron a Abuja

A cewarsa, yajin aikin da kungiyar ke yi na dakusar da harkar ilimin manyan makarantun gaba da sikandire, wanda hakan kan sa gwamnati ta rage sa kudi a fannin, duk da cewa Buhari yace ba Haka suke fata ba.

Buhari
Kungiyar ASUU Bata Da Wasu Dalilai Masu Kwari Na Ci Gaba Da Yajin Aiki - Buhari Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya nuna cewa barazanar cin hanci da rashawa a harkar ilimi tun daga matakin farko har zuwa manyan makarantun gaba da sakandire ne ke kawo cikas ga ƙokarin da muke. Kuma hakan nada alaƙa da dalilai mara sa rauni da ƙungiyar ke maƙalewa wajen tafiya yajin aikin.

Ya ce,

Kara karanta wannan

Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari

“Tsarin cin zarafin jinsi a makarantun na ƙara ƙamari. Baya ga Sauran nau'o'in cin hanci da rashawa da suka hada da biyan albashi a ma'aikatan bogi, yadda malaman ke ziyartar makarantun kudi wanda bana gwamnati ba fiye da biyu ko uku. Baya ga yadda malaman ke rubuta takardun taron karawa juna sani, rubuce-rubucen ƙwarewa ga akan wani ƙudi
“Na yi farin cikin yadda ICPC ke bincike tare da hukunta cin zarafin mata a manyan makarantunmu. Na goyi. Bayan haka. kuma na karfafa musu gwuiwa da su ci gaba da yin hakan. "

A ƙarshe, ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa ilimi a cikin kudaden shigan da ake samu, amma yace "dole ne masu ruwa da tsaki, da kafofin watsa labarai, da sauransu su bada shawara game da nuna yiwuwar yin gaskiya a fannin kashe ƙudaden da ake sawa a fannin ilimi, da kuma ƙuɗaɗen da ake samu a makarantun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel