FG ga ASUU: Ku Mutunta Umarnin Kotu, Ku Tattara ku Koma Aji

FG ga ASUU: Ku Mutunta Umarnin Kotu, Ku Tattara ku Koma Aji

  • Gwamnatin Buhari ta gargadi kungiyar ASUU ta da bi umarnin da kotu ta ba ta na gaggauta janye yajin aiki
  • Gwamnati ta zargi ASUU da rashin gaskiya tare da daura dalibai, mambobinsy da iyayen dalibai a turbar tsanar gwamnati
  • ASUU ta shiga yaji tun watan Fabrairun bana, ta shafe watanni sama da bakwai ba tare da karantarwa

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ja kunnen Kungiyar Malaman Jami’a akan kin bin dokar Kotun Ma’aikatun Kasa ta Najeriya (NICN) na ta koma kan aikinta daga dogon yajin aikin da ta ke yi.

Chris Ngige, Ministan Kwadago da Ayyuka, ya ce Kungiyar tana kera wa ‘yan Najeriya karya akan batun cikashe fom din daukaka karar akan umarnin kotu, rahoton TheCable.

An kirayi ASUU ta janye yajin aiki
FG ga ASUU: Ku Mutunta Umarnin Kotu, Ku Tattara ku Koma Aji | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya yi kira ga kungiyar akan ta mutunta umarnin kotun, ta kuma koma kan aikinta yayin da su ke kokarin ganin sun sasanta akan sauran matsalolin.

Kara karanta wannan

Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola

Ministan ya yi wannan batun ne ta wata takarda ta ranar Lahadi wacce ya Olajide Oshundun, mataimakin darektan sakin labaran Ministan ya sanya hannu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Kungiyar ba ta fadin asalin gaskiyar yadda aka yi da ita ga mutanen gari da kuma mambobinta, dangane da batunta na daukaka kara bisa umarnin da NICN ta bata ranar 2 ga watan Satumba, duk da bata yi hakan ba,” a cewarsa.
“Sai dai ASUU ta bukaci a ba ta damar daukaka kara. Sannan ta hada wannan bukatar tata da kuma takardar daukaka karar da ta ke da biyar yi da zarar an bata wannan damar.
“Har yanzu ba a riga an duba wannan bukatar ta ASUU ba. Don haka daga ina ASUU take?”

Ku Janye Yajin Aikin Nan Don ’Ya’yanmu Mu, Kakakin Majalisa Ya Roki ASUU

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Ta Nemi Yafiya Daga Yan Najeriya Kan Rashin Tsaro A Kasa

A wani labarin, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai a Najeriya ya yi kira ga kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU da su duba tare da janye yajin aiki saboda biyan muradan dalibai a kasar.

Ya bayyana hakan ne yayin dagawa da ASUU, ministan kwadago Chris Ngige da mukaddashin akanta janar na kasa Okolieaboh Sylva a jiya Alhamis 29 ga watan Satumba.

Kakakin na majalisa ya ce an biya bukatar majalisar a yanzu kam, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel