Asirin Likitan Bogi Ya Tonu Bayan Ya Kashe Tsohon Shugaban Gunduma Na APC a Bauchi Yayin Masa Tiyata

Asirin Likitan Bogi Ya Tonu Bayan Ya Kashe Tsohon Shugaban Gunduma Na APC a Bauchi Yayin Masa Tiyata

  • Jami'an tsaro a jihar Bauchi sun kama wani Andrew Godwin da ake zargi likitan bogi kan halaka wani majinyaci yayin tiyata
  • Rahotanni daga garin Bogoro sun bayyana cewa Godwin ya shafe shekaru yana yi wa mutane da ba su ankare ba tiyata kuma daga bisani su mutu
  • Bincike ya nuna cewa Andrew yana da kemis na sayar da magunguna amma ba shi da lasisi ko satifiket na yi wa mutane tiyata

Jihar Bauchi - Jami'an tsaro na hadin gwiwa ta Base 14 Boi a karamar hukumar Bogoro sun kama wani Andrew Godwin da ake zargin likitan bogi ne a Bauchi, Nigerian Tribune ta rahoto.

An kama wanda ake zargi likitan bogin ne, dan asalin jihar Nasarawa a ranar Lahadi saboda yin tiyata wacce ba ta yi nasara ba ta kuma yi sanadin mutuwar wani Joshua Haruna, dan shekara 45 mazaunin Gambar Lere a karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Likitan Bogi
Asirin Wani Likitan Bogi Ya Tonu A Bauchi Bayan Ya Kashe Majinyaci Yayin Tiyata. Hoto: @NigerianTribune.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin, wanda ya shafe shekaru yana zaune a Gambar Sabon Layi a Tafawa Balewa ya dade yana haramtaciyyar kasuwancinsa kan mutane da ba su ankare ba.

Likitan bogin yana sayar da magunguna ne amma ba shi da wani satifiket na likitanci ko izini daga hukumomin da suka dace don ya rika tiyata.

An ce ya bude cikin wani majiyanci kuma ya bar shi a bude har ya goben ranan.

Mutanen gari sun ce Andrew ya dade yana yi wa mutane tiyata suna mutuwa

Wani rahoto da ba a tabbatar ba ya ce Mr Andrew Godwin ya dade yana yi wa mutane tiyata wanda ba a samun nasara kuma daga bisani su mutu sakamakon tiyatar.

Jami'in JTF da ya kama shi ya ce sun kama ma'aikacin lafiyar na bogi sun kuma mika shi hannun yan sanda na Bogoro don zurfafa bincike.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yaro karami ya nutse a tafki a wata jihar Arewa

An mika Andrew hannun yan sanda don cigaba da bincike

An tura binciken zuwa caji ofis na yan sanda a Tafawa Balewa saboda Gambar Sabon Layi na karkashin karamar hukumar Tafawa Balewa ne yayin da Gambar Lere na karamar hukumar Bogoro.

Mamacin, kafin rasuwarsa shine tsohon shugaban gunduma ta APC, Boi C a karamar hukumar Bogoro kuma shugaban kamfen na Sanata Lawal Yahaya Gumau.

Wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi wata mata da ke zaune a Bogoro a jihar Bauchi wacce ta yi karin haske kan Godwin.

Matar, wacce ta nemi a sakayya sunanta saboda dalilan tsaro ta ce kimanin tsawon shekaru uku sun san shi yana sayar da magani amma ba su san yana tiyata ba.

Ta ce:

"Gaskiya mafi yawancin mutanen gari ba su cika iya banbance likita mai lasisi ba da sauran ma'aikatan bangaren lafiya.
"Su dai idan sun ga mutum ya bude kemis ko kuma suna ganinsa a asibiti sai ka ji suna kiransa dakta/likita ko yana sayar da magani a unguwa."

Kara karanta wannan

Budurwa ta shiga damuwa, ta hada kayataccen biki amma kawayenta suka ki hallara

Ta kara da cewa mutane da dama suna zuwa wurinsa magani su samu matsala amma da ya ke ba fitattun mutane bane maganar na mutuwa.

An kama sojan gona da kayan hukumar FRSC dauke da katin shaidar aikin soja a Kano

A wani rahoton, Jami'an hukumar kiyaye hadura na kasa (FRSC) da hukumar yan sanda sun kama wani mutum mai suna Injiya Gude Ude a jihar Kano da kayan jami'an hukumar kiyaye hadura FRSC kuma dauke da katin shaidar aikin sojan a garin Kano.

Sanarwan da hukumar FRSC ta bayar mai dauke ta sa hannun mukadashin Secta Kwamanda, Ahmed T. Mohammed ta cean kama Ude ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairun 2018 a titin Kaduna - Kano a yayin da rundunar ke gudanar da wata kewaye na musamman da akayi wa take da "Operation Zero"

Asali: Legit.ng

Online view pixel